Abin da ya sa muka hana Buhari ciyo bashi - Shehu Sani

Sanata Shehu Sani Hakkin mallakar hoto @shehusani

Bukatar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tura wa majalisar dattawa domin ta amince ya ciyo bashi ta fara janyo ce-ce-ku-ce.

Shugaban ya sake tura bukatar neman karbo bashin kusan dala biliyan 30 bayan ya fuskanci tirjiya a majalisa ta takwas, wa'adin mulkinsa na farko.

Buhari wanda ya ce yana bukatar bashin domin gudanar da ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ke yi, ya fadi a wasikar da ya aika wa majalisa cewa yana bukatar ciwo bashin saboda wani bangare ne kawai majalisa ta takwas ta amince da shi.

Kuma Sanata Sahabi Ya'u mataimakin mai ladabtarwa bangaren marasa rinjaye a majalisar dattawa ya ce dama shugaban yake nema ya yi amfani da bashin da majalisa ta takwas ta amince ya karbo.

Sai dai kuma Majalisa ta takwas ta ce ta yi watsi da bukatar shugaban ne saboda dimbin bashin da ke kan Najeriya da kuma rashin cikakken bayani kan hanyoyin da za a bi wurin biyan basukan.

Sanata Shehu Sani shugaban kwamitin kula da basuka a majalisa ta takwas ya ce Lokacin da gwamnatin APC ta hau mulki a 2015 ana bin Najeriya dala biliyan 10 da miliyan 32.

"Kuma a cikin shekara uku gwamnatin Buhari ta ciyo bashin dala biliyan 11 da miliyan 77, idan aka hada da tsohon bashi ya zama dala biliyan 22 ake bin Najeriya."

"Idan muka yarda gwamnati ta sake ciyo bashin biliyan 30 zai zama ana bin Najeriya bashin biliyan 50," in ji shi.

Ya kara da cewa dalilin da ya sa suka hana a ciyo bashin, shi ne zai yi wahala a iya biyan bashin har a yi wasu ayyukan ci gaba.

Amma a bukatar cin bashin da Buhari ya sake aikawa domin neman amincewar majalisa ya ce zai karbo bashin ne saboada kammala wasu ayyukan gwamnatinsa da ke cikin kudirin 2016-2018.

Hakkin mallakar hoto Buhari Sallau

Shugaban ya ce ayyukan da rashin amincewa da kudirin ya shafa sun hada da hakar ma'adanai da wutar lantarki da lafiya da noma da ruwan sha da kuma ilimi.

Sanata Shehu Sani ya ce ya kamata ace 'yan Najeriya sun ga canji daga basukan da kasar ta ciyo a baya.

"Shin daga wancan lokaci da aka ciyo bashi zuwa yanzu, halin rayuwa na 'yan Najeriya ya inganta? Shin talakan Najeriya na cikin jin dadi koko komi ya yi sauki kuma yana tafiya cikin sauki?"

Labarai masu alaka