Yadda kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi a Najeriya

BBC

Da alama wasu daga cikin 'yan Najeriya na dandana kudarsu sakamakon tashin gwauron zabi na kayayyaki musamman na masarufi a kasar.

Hauhawar farashin bai rasa nasaba da rufe iyakokin kan tudu na kasar da aka yi a kwanakin baya inda jami'an hana fasa kwabri tare da hadin gwiwar wasu jami'ai masu kayan sarki ta kasar ke sintiri ta kan iyakokin kasar domin tabbatar da an dakatar da shigo da kayayyaki.

Ko a kwanakin baya sai da Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta shaida cewa rufe iyakokin Najeriya ya bada gudunmawa wajen tashin farashin kayayyaki a kasar.

Ministar ta ce cikin wata biyu kacal, an samu hauhawar kayan ne da kaso 11 da digo 60 cikin 100.

A dalilin hakane BBC ta gudanar da bincike a wasu kasuwanni a Najeriya kan yadda kayayyakin suka yi tashin gwauron zabi tun daga watan Janairun 2019 zuwa Nuwamba.

Farashin kayayyaki a watan Janairun 2019 zuwa Nuwambar 2019 (Daga kasuwar Singa Kano)

  • Buhun Shinkafa ('Yar gwamnati) N14,000 - N19,200
  • Buhun Shinkafa ('Yar gida) N13,500 - 18,500
  • Buhun Semovita N2,900 - N3,100
  • Kwalin Taliya (Silver) N3,100 - N4,500
  • Kwalin Taliya Golden Penny N3,200 - N3,650
  • Man Gyada (25 liters) N9,000 - N11,800
  • Buhun Masara N5,000 - N9000
  • Wake Mudu Daya N250 - N500
  • Buhun Gero N8000 - N11,000
  • Buhun Suga N13,500 - N13,500

Sai dai bayanai sun nuna cewa buhun suga ne kadai bai kara kudi ba a cikin irin wadannan kayayyakin.

Wane hali mutanen Najeriya ke ciki?

Tsadar abinci ko kayayyakin masarufi a Najeriya ba sabon abu bane, domin tun a baya akan samu hauhawar kayayyaki, a wani lokaci kuma su sauka wasu kayayyakin kuma idan suka hau shikenan sai kuma abin da Allah ya yi.

Wasu daga cikin 'yan kasar na bayyana cewa suna da yakinin cewa rufe iyakokin kasar alheri ne ga kasar sakamakon suna da yakinin cewa nan gaba za a ga amfanin hakan.

A wani bangaren kuma wasu na kokawa kan hauhauwar farashin inda suke nuna cewa gari ya yi zafi a halin yanzu a Najeriyar.

A shafin Twitter, Abubukar Aliyu na ganin cewa rufe iyakokin kasar ci gaba ne, kuma nan gaba kasar za ta ga amfanin hakan.

Shi kuma Alhaji Abdullahi Sarkin Baka ya nuna da alama talakan kasar na cikin wani mawuyacin hali.

Farashin kayan abinci a Najeriya

Kayan AbinciJanairu 2019Nuwamba 2019
Buhun shinkafa 'yar waje14,00019,200
Buhun shinkafa 'yar gida13,50018,500
Samobita2,9003,100
Taliya Silva3,1004,500
Taliya Golden Penny3,2003,650
Man gyada lita 259,00011,800
Buhun masara5,0009,000
Wake mudu daya250500
Buhun gero8,00011,000
Buhun suga13,50013,500
Bayanai: Kasuwar Singa Kano

Me masana tattalin arziki ke cewa?

Kan wannan batu na hauhawar farashin kayayyaki, BBC ta tattauna da dakta Shamsuddeen Muhammad, masani kan tattalin arziki kuma malami a Jami'ar Bayero da ke Kano.

Ya bayyana cewa wannan hauhauwar farashi abu ne da zai kara talauci kan talauci da talakan Najeriya yake ciki.''

Malamin ya ce ko a kwanankin baya wata kididdiga ta nuna cewa Najeriya ce kasar da ta fi ko wace kasa ''yawan talakawa a duniya.''

Ya ce a bana gwamnatin kasar ta ce tana hasashen hauhawan farashin ba zai wuce kashi 9.98 cikin 100 ba sai ga shi kuma ya kai kusan kashi 12.

Dakta Shamsuddeen ya bayyana cewa da alama gwamnatin kasar ba ta yi aikinta yadda ya kamata ba wajen wannan hasashen.

Mece ce mafita?

Dakta Shmasuddeen ya bayyana cewa ''ta inda aka hau ta nan ake sauka.

Ya ce gwamnatin kasar ta san alkaluman da ta taba wadanda suka jawo hauhawar farashi.

''Babu yadda za ayi kasar da ba ta noma cikakken abincin da za ta ci kuma a ce an hana shigo da abinci.''

Ya ce duk kasar da ta yi haka za a samu hauhawar farashi ko da na gajeren lokaci ne a cikin kasar.

Ya ce mafita a nan ita ce gwamnati ta koma ta kara duba dokokin da ta yi na rufe iyakoki da kuma haraji da aka saka mai tsanani na shigo da kayan abinci cikin kasa musamman shinkafa.

Labarai masu alaka