Sauye-sauye da takurawa na yin kan-kan-kan a Saudiyya

Filin wasa da ke Riyadh a kasar Saudiyya Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kasashen Brazil da Argentina sun buga wasan kwallo a cikin fiilin wasa da ke Saudiyya kuma 'yan kallon maza da mata ne

Tsagerun matasan na can mazaunin da ke saman babban filin wasan kwallon kafa da ke birnin Riyadh, sun cire rigunansu suna dagawa sama tare da fito da dariya kamar dai yadda a kan gani a filayen wasa.

A bangare guda kuma gungun matan Saudiyyar ne ke irin nasu salon na jin dadin samun 'yancin da ba a taba samu ba a tarihi, dankwalinsu na yawo a sararin samaniya tamkar bakar tuta.

Wasan kwallo da aka yi tsakanin Brazil da Argentina shi ne na farko da na taba zuwa kallo a kasar Saudiyya cikin sama da shekara 20.

A wancan lokacin wadanda za ka gani a wajen kallon zaratan mazan kasar ne sanye da farar jallabiya, da bakin kwarkwaron da aka nade shi da farin mayafi, ko launin fari da ja, a wancan lokacin babu macen da ta isa zuwa wannan waje balle ka ga giftawar bakar riga ko dankwali.

A wancan lokacin birnin Riyadh ya kasance wuri maras dadin sha'ani, mutanen cikinsa ba sa haba-haba da jama'a, babu wani abin da zai dauki hankalin ka baya ga dogayen fitilun da suke ciki da wajen manyan shagunan sayar da kayayyaki.

Da ka shiga birnin babu wata iska mai dadi da za ka shaka saboda rashin dadi, tamkar ka nutse cikin kwamin wanka alhalin ba ka iya ninkaya ba, babu wani abu da za a kira zamani ko wurin shakatawa da za ka ga cakuduwar maza da mata.

Hatta lokacin da ka je yin sayayya manyan shaguna, matukar lokacin sallah ya gabato dukkan masu wajen dole du rufe, wannan doka ce mai karfin gaske a daukacin kasar wadda kuma ake bin ta sau da kafa.

Idan ka kuskure 'yan sanda suka samu shagonka a bude a lokacin sallah, kashinka ya bushe don kuwa za su rufe shi, a tasa keyarka zuwa wajen hukuma don fuskantar hukunci.

Ga matasan Saudiyya kuwa, rayuwar sai sannu, duniyarsu baki daya ta kare ne a cikin gidajen alfarma masu dogayen katanga wadanda ake fadadawa a kowacce shekara idan an samu faragar mallakar wani fili da ke kusa, hatta ziyara ta kare ne a gidan 'yan uwa shakikai na jini.

Amma a yanzu wannan ya zama tarihi, Riyadh ta sauya

Image caption An dauki hoton fitattun mawaka larabawa a wani bidiyo da suke tallan manyan wurare a birnin Riyadh

Sauye-sauyen da aka fara samu, da rage takurawa walwalar jama'a da bacewar 'yan sandan da ke cafkewa da garkame shagunan wadanda ba su rufe a lokacin sallah ba ya kawo sauyi ga rayuwar 'yan kasar.

Wata ruwa biyu 'yar Saudiiya, da ta mayar da kanta mai kayan kawa na mata, ta shaida min lokacin da mutane irinta ya haramta su bayyana baiwar da suke da ita.

Ta ce sauyin da aka samu yanzu da ta dawo kasar, ya sanya tana kallon kanta kamar wata 'yar kauye idan ta kwatanta da kawayenta da ke cikin kasar saboda 'yancin da suka samu.

Dan mabudin sauyin rayuwar matan kasar ya samo asali daga fara ba su dama da 'yancin tukin mota a shekarar da ta gabata, duk da cewa har yanzu ita kanta ba ta samu lasisin tuka motar ba.

A yanzu kawayentaa sun samu 'yanci, suna tafiya kafada da kafada da maza.

Image caption Manyan shaguna da aka kawata da tallan mawaka maza da mata na jan hankali sosai a Riyadh

Na yi tuya na manta da albasa, ban yi batun mata masu fafutuka su hudu na kasar da ake tsare da su a gidan kaso ba, kai har da wasu karin mutum bakwai da aka ba da belinsu ba.

Kuma su ne kashin bayan wannan 'yanci da ake ganin mata sun samu a Saudiyya wadanda ake zargi da yi wa jami'an tsaro tsageranci, da kuma kafafen yada labaran kasar suke kira da sun ci amanar kasa.

Azabar da suke ciki tamkar wani tabo ne a jikin fatar sabuwar Saudiyya da mata suka fara samun 'yanci, sai dai fa hakan ba ya na nufin an samu ainahin sauyin da ake batu.

Wannan ita ce babbar matsalar, abubuwa da dama na faruwa amma ba lallai a san da su a sarari ba.

Daukacin birnin Riyadh ya samu 'yancin walwala da nishadi cikin watanni biyu irin wanda ba a taba gani ba.

An bude gidajen kallon wasanni daga na kwallon kafa har da na dambe, sai uwa uba wasan da mawaka Turawa suka yi a kasar.

A lokacin da nake kallon yadda mawakan ke cashewa, mawakin salon rap dan Amurka ya jefa wa 'yan kallo rigar nono, wannan bidiyon ya zagaya duniyar shafukan sada zumunta.

Akwai wani kebantaccen wuri a birnin Riyadh mai suna Boulevard, da aka kawata da manyan fitilu da yake daukar hankalin dubban mutane a kowanne dare.

Hotunan fitattun mawakan Larabawa aka jera kan babban titi, inda matasa 'yan matan Saudiyya da ke rufe ruf da doguwar riga da mayafi suke tsayawa kallo cike da sha'awa da nishadin sabon sauyin da suka samu.

Wasu na tsayawa kantinan da suke sayar da turaruka don sansanawa, wasu mata sanye da nikabin rufe fuska suna gefe guda suna nishadantar da jama'a da kidan goge, ga kuma wata motar sayar da abinci.

Akwai wuraren sayar da abinci kala-kala da maza da mata ke zuruftu a ciki, wanda a baya ba su isa yin tafiya kafada da kafada ba matukar ba muharraman juna ne ba.

Ana gudanar da wasanni daban-daban na nishadantarwa, an kayata wurin da abubuwan ban sha'awa inda ake gudanar da wasan dabe duk bayan sa'a guda.

Image caption Har yanzu akwai dokar sanya suturar kamala kan matan Saudiyya

Shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata, idan aka ce za a ga irin wadannan abubuwan a kasar Saudiyya wani ba zai yadda ba, wadda kasa ce da ke cike da manyan malaman addinin musulunci wadanda suke da karfin fada a ji, amma yanzu an fara rage musu karfi.

Yawancin malaman dai suna gidan kaso, wandan suka ki bin yarima su sha kida. Ma'ana wadanda ba su amince da sauyin da Yarima Muhammad bin Salman mai jiran gadon masarautar ya shigo da su ba.

Ina daga cikin daruruwan 'yan kasar da suka taru a babban masallacin da ke Riyadh don zaman makokin daya daga cikin malaman da ake tsare da su a gidan kaso.

Masu fafutuka sun dora alhakin mutuwarsa kan mahukunta kan azabtar da shi da suka yi a lokacin da yake gidan kaso duk da cewa ba a tabbatar da hakan ba.

Kwanaki kadan kafin mutuwarsa, birnin Riyadh ya kadu matuka sakamakon wani mahari da ya dabawa mawakan Turawan wuka da suka zo don nishadantar da 'yan Saudiyyar tare da ji musu mummunan rauni.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A shekarar 2017 Sarki Salman ya nada dansa Muhammad bin Salman yarima mai jiran gado

Ma'aikata da masu bai wa Yarima Mohammed bin Salman sun ce wannan dalili ne ya sanya duniya ta bi shi a sannu, sakamakon karfin ikon da yake da shi.

Ina birnin Riyadh a shekarar da ta wuce, don daukar rahoto kan kisan dan jarida kuma dan kasar Jamal Khashoggi da manyan jami'an Saudiyya suka aikata a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul a kasar Turkiyya.

Wani editan kasar ya shaida min labarin abin da ya faru na mamaki ne da irin bayanan da suke ta fitowa da kuma wasu suka zama gaskiya.

Wannan kisa ya sanyaya gwiwar manyan shugabannin kasashen waje, da suka yi kokarin kauce wa zuwa Saudiyya a wannan lokacin.

Har yanzu abin tsoro da sarkakiyar da ke cikin mutuwar dan jaridar, na sanya shakku kan wannan sauyin da aka samu a abin da duniya ke kira sabuwar Saudiyya.

Labarai masu alaka