An kama masu garkuwa da yara a Kebbi

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Atiku Bagudu kan batun satar yara

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar Atiku Bagudu da Yusuf Yakasai

Hukumomi a jihar Kebbi sun bayyana cewa an sake gano wasu kananan yara biyu da aka sace daga jihar wadanda ake zargin an yi safararsu zuwa kudancin Najeriya.

Ko a watan jiya ma sai da gwamnatin jihar ta mika wasu yara hannun iyayensu bayan jami'an tsaro sun gano su daga hannun masu satar yaran.

Batun satar kananan yara ana safararsu zuwa kudancin kasar, ya yi matukar tayar da kura kwanan baya lokacin da 'yan sanda suka gano wasu yara 9 da aka yi zargin an sace su daga jihar Kano zuwa kudancin kasar.

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya yi wa BBC karin bayani inda ya bayyana cewa an yi nasarar kubuto yaran da aka yi garkuwa da su daga yankin Zuru, kuma an yi nasarar kama wasu da ake zargin suna garkuwa da yara.

Ya ce hukuma na rike da wata mace da ake zargi da satar yara mai suna Uchenna da kuma wata mai suna Agatha da wani mai suna Samson da kuma wani mai suna Moses.

Ya ce wadanda aka kama din suna hannu kuma suna taimaka wa hukuma wajen bincike da ake yi na wannan lamari.

Gwamnan ya ce hukumar tsaro ta farin kaya na nan na bincike kan kararraki da aka kawo na yaran da suka bata.

Labarai masu alaka