An haramta aika sakon waya idan ana tuki

Direba na aikawa da sakon murya alhalin ya na tuki
Image caption Duk direban da aka kama da karya dokar za a ci shi tara

A kasar Australia an kafa na'urar daukar hoton fasaha da nufin gano direbobin da ke aikawa da sakon wayar salula alhalin suna tukin mota.

An kaddamar da sabuwar fasahar ne a ranar 1 ga watan Disamba, kuma duk direban da aka samu da laifi a watanni ukun farko da fara amfani da fasahar za gargade shi. Amma idan ya sake aikatawa za a ci shi tara.

Gwajin farko da aka fara a rubu'in karshe na shekarar 2019, ya dauki hotunan sama da direbobi 100,000 da suke amfani da wayar salula a lokacin tuki.

Ministan da ke kula da hanyoyi Andrew Constance ya ce ''Yawancin mutane ba su samu sakon wayar salula da muka aika ba kan sabuwar dokar da kuma hadarin amfani da ita idan su na tukin mota.''

Ya kara da cewa idan suna karanta sakonnin da ake aikawa na kar ta kwana kan muhimmancin daina amfani da wayar salula idan suna tuki, za su fahimci cewa amfanin kansu ne da fasinjojin da ke cikin motar har da al'umar yankunansu saboda hadarin da hakan ke janyowa.

Ana sa ran fadada sanya fasahar zuwa yankuna 45 na Australia nan da shekarar 2023, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Haka kuma sun bayyana cewa wannan ita ce fasaha irinta ta farko da aka fara amfani da ita a duniya.

Sannan an yi mata tsarin da za ta iya aiki a kowanne yanayi, ko sanyi, ko zafi ko lokacin damuna har da lokacin zubar dusar kankara.

Labarai masu alaka