'Yar Australia ta kubuta bayan makalewa a cikin ruwa

Tamra McBeath-Riley tare da karenta Raya Hakkin mallakar hoto NT Police
Image caption Tamra McBeath-Riley tare da karenta Raya sun je wurin shan ruwan dabbobin a cikin mota

An yi nasarar kubutar da wata mace da ta ce ta shafe kwana 12 tana cin biskit da shan ruwa bayan ta gano wurin da dabbobi ke kiwo da shan ruwa.

Matar mai suna Tamra McBeath-Riley tana tare da wasu mutum biyu a lokacin da motarsu ta makale a gabar ruwa.

Tawagarsu ta rabu ne don neman taimako.

An gano Mis McBeath-Riley a kusa da motar amma kuma sauran mutanen sun bace.

'Yan sanda sun ce tabbas za su galabaita sakamakon rashin ruwa har na kwana 13.

'Ruwan shan dabbobi ya taimaka mu su'

Da sassanyar ranar 19 ga watan Nuwamba ne matar, mai shekara 52, sun yi tafiyar ne tare da wasu mutane biyu Claire Hockridge da Phu Tran, zuwa garin Alice Springs da ke arewacin kasar Australia.

Sun yi tafiyar tare da karen Mis McBeath-Riley's mai suna Raya, da kuma wata mace ma'aikaciya.

Suna tafiyar ne a yankin mai sarkakiya da ke kusa da yankin Alice Springs a lokacin da motarsu ta makale a bakin ruwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Garin Alice Springs na daga cikin manyan garuruwan da ke yankin arewacin Australia

Da take magana da manema labarai a asibitin da aka kwantar da ita, McBeath-Riley ta ce sun yi kwana uku a kusa da motar suna ta kokarin ganin sun fitar da ita, amma lamarin ya ci tura.

"Mun yi kokarin fita daga wajen amma lamarin ya ci tura, saboda ruwan yana da fadi," in ji ta.

''Ana tsananin rana a wajen, don haka sai mu shige cikin motar mu fake. Haka da daddare a cikin motar muke barci.''

Sun cinye duk dan guzurin da suka taho da shi, ciki har da ruwan sha na gora, da biskit, da barasa, da taliya.

Bayan ruwan shansu ya kare, sai suka gano wani wuri da dabbobi ke shan ruwa. Sai suka rika diban ruwan suna tafasawa tare da tacewa da riga kafin suka sha.

"Duk da haka ruwan ba shi da tsafta, bai dace a sha ba, amma duk da haka shi ne ya sanya suka rayu.''

Sufuritandan 'yan sanda na yankin Pauline Vicary ya shaida wa kafar yada labaran kasar.

Daga bisani sai suka yanke shawarar su rarrabu dan neman taimako, inda Mista Tran da Mis Hockridge suka yanke shawarar su bi babbar hanya.

Ita kuma McBeath-Riley sai ta tsaya a wajen motarsu, saboda tunanin karenta Raya ba zai iya doguwar tafiya ba.

'Yan sandan yankin sun bazu cikin dajin tare da jirage masu saukar ungulu don neman mutanen.

Sun yi nasarar gano Mis McBeath-Riley a nisan kilomita daya da rabi daga inda motarsu ta makale bayan wani mazaunin yankin ya kai rahoton ganin alamar tayar mota a wajen.

"Tana cikin dimuwa saboda lokacin da suka shafe a daji. Alamu sun nuna ta dade a inda ruwan yake, kuma shi ne ruwan da take sha. Ta yiwu wannan ya sanya ta tsira da ranta,'' inji 'yan sandan.

An kai McBeath-Riley asibiti don ba ta taimakon gaggawa sakamakon gurbataccen ruwan da ta sha.

Ta ce ta yi tunanin an gano inda abokan tafiyarta suke, amma yanzu da ta samu labarain ba'a gansu ba, abin yana damunta.

Tuni 'yan sanda suka fara neman inda suke, inda za a fadada aikin zuwa shiga dajin da kafa.

Wani jami'in dan sanda da kafar yada labarai ta ABC ta yi hira da shi, ya ce yankin wuri ne mai sarkakiya da baudaddiyar hanya, amma duk da haka suna kokarin fara binciken, baya ga amfani da jirgi mai saukar ungulu.

Labarai masu alaka