Ganduje ya aika wa majalisa sabon kuduri kan sabbin masarautu

Salihu Tanko Yakasai Hakkin mallakar hoto Salihu Tanko Yakasai

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aikawa da wani sabon kudiri ga majalisar jihar, domin kafa sabbin masarautu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta jihar ta sake aika wani sabon kudiri da zai bayar da damar kafa masarautar Rano da Gaya da Bichi da kuma Karaye.

Kwamishinan ya bayyana cewa an gyara kudirin dokar masarautu ta 2019 ne saboda gyaran ya shafi jama'a.

Barista Ibrahim Mukhtar shi ne lauyan bangaren gwamnatin jihar, kuma ya shaida wa BBC cewa kotu ta yanke hukuncin ne ba tare da tsayawa ta yi bincike yadda ya kamata ba.

Waiwaye

A ranar Alhamis 21 ga watan Nuwamban 2019 ne babbar kotun jihar ta rushe dokar da ta bai wa majalisa damar kirkiro sabbin masarautun.

Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.

Hukuncin na nufin yanzu sarki daya ne a Kano ba biyar ba kamar yadda aka kirkira a 'yan watannin da suka gabata. Amma wannan sabon kuduri zai iya sauya hukuncin kotun kamar yadda masu sharhi ke cewa.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin jihar ta Kano ta kirkiro da sabbin masarautun na Kano inda jim kadan bayan kirkirar masarautun, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da takardar kama aiki ga sabbin sarakunan.

Sarakunan da aka bai wa takardun sun hada da Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Bichi, da kuma Dakta Ibrahim Abubakar a matsayin Sarkin Karaye sai Tafida Abubakar Ila a matsayin Sarkin Rano da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir a matsayin Sarkin Gaya.

Kirkirar masarautu a Kano ya jawo ce-ce-ku-ce a jihar da Najeriya gaba daya inda aka samu mabanbantan ra'ayoyi.

Labarai masu alaka