Kulle iyakoki: 'Ana samun ci gaba a Najeriya'

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ministan watsa labarai da al'adu Lai Mohammed ya bayyana cewa an samu ci gaba matuka sakamakon kulle iyakokin kasar da aka yi.

Ministan ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kai a iyakar Najeriya da Nijar da ke Magama a Jibiya jihar Katsina.

Ministan ya bayyana cewa a kwanakin baya tawagar gwamnatin kasar ta kai ziyara iyakar Seme, cikin wadanda suka kai ziyarar har da ministan watsa labarai tare da mataimakin shugaban hukumar kwastam, da ministan harkokin cikin gida da shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasar.

Lai Mohammed ya bayyana cewa an kaddamar da atisayen nan mai suna 'SWIFT RESPONSE' ne a matsayin daya daga cikin matakai da Najeriya ta dauka na tsaftace iyakokinta.

Atisayen dai na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar kwastam da ta shige da fice da rundunar sojojin kasar da 'yan sanda da kuma sauran jami'an kasar masu kayan sarki.

Ya bayyana cewa rashin bin ka'idoji da yarjeniyoyi da Najeriyar ta yi da makwabtanta na daga cikin abubuwan da yasa Najeriyar ta dauki wannan mataki.

Lai Mohammed ya ce tun bayan kulle iyakokin kasar, an samu ci gaba ta fannin rage fasa kwabrin kayayyaki musamman shinkafa, kuma kasar ta samu karin kudin shiga ta bangaren shigo da kayayyaki da kusan kashi 15 cikin 100.

Ya ce kulle iyakokin ya kawo sauki da shigo da kananan makamai da kuma shiga kasar da baki ke yi ba bisa ka'ida ba.

Ya ce ba wai an kaddamar da wannan atisayen ba ne domin karya tattalin arzikin wata kasa ko kuma wani yanki kamar yadda ake yadawa.

Ministan ya tabbatar da cewa kasuwanci a cikin Najeriya ya kara habaka musamman fannin noma, inda manoman shinkafa ke samun babban rabo.

Labarai masu alaka