Wutar lantarki ta kashe fursinoni a Legas

Minister of Interior Rauf Aregbesola land Ikoyi prison to chook eye for di mata
Image caption Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Rauf Aregbesola ya kai ziyara gidan yarin a ranar Litinin

Wutar lantarki ta yi ajalin wasu fursinoni a wani gidan yarin unguwar Ikoyi da ke jihar Legas a ranar Litinin, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Shugaban Hukumar da ke Kula Gidajen Yari a Najeriya Ahmed Ja'afaru ne ya tabbatarwa BBC wannan labarin.

Ya ce al'amarin ya faru ne misalin karfe 7 na safe, sai dai bai yi karin haske ba dangane da abin da ya jawo al'amarin.

Kodayake wani ma'aikacin gidan yarin ya ce al'amarin ya faru ne bayan karuwar karfin wutar lantarki a gidan yarin.

Kamar yadda ganau suka bayyana, sun ce al'amarin ya faru ne bayan wata wayar lantarki ta tsinke kuma ta fada a kan wani gadon fursinoni yayin da suke barci.

Akalla fursinoni biyar ne suka rasa rayukansu kuma wasu da dama ne aka garzaya da su asibiti bayan sun ji raunuka.

Sai dai hukumomi sun ce sun fara gudanar da bincike kan al'amarin.

Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Rauf Aregbesola ya kai ziyara gidan yarin don gane ma idonsa abin da ya faru.

Labarai masu alaka