Matar Amitab Bachchan ta bukaci a kona wadanda suka yi wa wata fyade

Vigil in Amritsar 01/12 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi ta zanga-zanga a kasar

Wata 'yar majalisar dokokin Indiya Jaya Bachchan ta ce kamata ya yi a kona mutanen da suka yi wa wata matashiya mai shekara 27 fyade tare da yi mata kisan gilla a birnin Hyderabad.

Da take jawabi a majalisar, Jaya wadda matar fitaccen jarumin fina-finan Indiya ne Amitab Bachchan ta ce: "Na san kalaman nawa sun yi tsauri, amma irin wadannan mutanen kamata ya yi a fito da su bainar jama'a a kona su."

'Yan majalisa da dama sun yi Allah-wadai da fyaden da aka yi tare da kisan matashiyar.

An yi ta zanga-zanga a fadin Indiya bayan da aka gano gawar matashiyar tun bayan batanta a makon da ya gabata.

'Yan sanda sun ce sun kama mutanen hudu da suka yi wa matar fyade tare da kasheta.

Har yanzu fyade da cin zarafin mata na karuwa a Indiya duk da irin yadda ake nuna fushi da yin Allah-wadai a kansu.

A ranar Litinin, 'yan majailsa suka nuna fushinsu tare da bukatar sanin shirin da gwamnati ke yi don tabbatar da cewa an samar wa mata tsaro a kasar.

Ms Bachchan, wadda tsohuwar jarumar finan-finan Indiya ce, mai kuma kokarin nemar wa mata 'yancinsu, ta jagoranci 'yan majalisar don nemo wa matashiyar hakkinta.

"Ina ga lokaci ya yi... Mutane na son gwamnati ta bayar da gamshasshiyar amsa," a cewarta.

Vijila Sathyananth, wata 'yar majalisa daga kudancin kasar Tamil Nadu, ta ce babu tsaro ga mata da yara a Indiya, ta kuma bukaci "a rataye maza hudun da suka aikata fyaden kafin ranar 31 ga watan Disamba.

"Bata lokaci wajen yanke hukunci kamar tauye hakki ne," in ji ta.

Ministan tsaro Rajnath Singh ya ce wannan lamari ya jawo abin kunya ga kasar, ya kuma bakanta wa mutane rai, "har ma ba ni da kalmar da zan iya fassara lamarin da ita," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@aninews
Image caption Jaya Bachchan ta ce mutane na son gwamnati ta ba da sahihiyar amsa