EFCC ta gano makarantar koyar da zamba ta intanet

internet fraudster Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya EFCC ta ce ta kama wasu mutum 23 da aka bai wa horo kan zamba ta intanet a jihar Akwa Ibom.

Jami'an hukumar sun gano mutanen ne a wani gini da ake zargin masu zamba ta intanet ne suke amfani da shi wajen bai wa mutane horo kan yadda za su kware a harkar damfara.

Wajen yana kauyen Ikot Ibiok da ke karamar hukumar Eket ne ajihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwajaren ya fitar, ta ce an wadanda ake zargin suna tsakanin shekaru 19 zuwa 35 ne, kuma ana koya musu yadda za su dinga damfara da sata ta intanet.

Wannan shi ne waje mafi girma "na makarantar koyar da zamba" da EFF ta gano a kokarinta na hana zamba ta intanet.

EFCC ta ce an kama komfuta 34 da wayar hannu 21 a lokacin da aka kai samamen.

Za kuma a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

An bai wa mutane horo kan yadda za su yaudarar mutane ta yadda za su damfare su.

Suna ayyukansu ne ta hanyar bad da sawu ta hanyar shafe adireshinsu na intanet da amfani da layukan wayar da ba a yi wa rijista ba.