Zikrullah Olakunle: Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar Alhazai

getty images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sunan sabon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya da mambobinta ga majalisar dattijan kasar.

Majalisar dattawan kasar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karanta wata wasika da shugaban kasa ya turo mata kan nada sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya.

Sunan wanda shugaban kasar ya mika a matsayin wanda yake so a ba shi shugabancin hukumar Zikrullah Olakunle Hassan wanda ya fito ne daga jihar Osun.

Idan har majalisar dattijan ta tabbatar da nadin, to Olakunle ne zai gaji Abdullahi Mukhtar wanda ke kan kujerar tun 2015.

Wasu daga cikin wadanda shugaban ya mika sunayensu da za su zama kwamishinoni karkashin hukumar sun hada da Abdullahi Magaji Hardawa wanda ya fito daga Bauchi, sai kuma Nura Hassan Yakasai wanda ya fito daga jihar Kano.

Akwai kuma Sheik Momoh Suleman Imonikhe wanda ya fito ne daga jihar Edo.

Abdullahi Mukhtar ya jagoranci hukumar alhazai tun watan Mayun shekarar 2015 jhar zuwa yau da aka nada sabo.

Labarai masu alaka