Taron Nato: Trump ya caccaki Macron kan Nato

President Donald Trump attends a meeting with Nato Secretary General Jens Stoltenberg (not pictured), ahead of the summit in London, Britain, December 3, 2019 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bana kungiyar kawancen tsaro ta Nato take cika shekara 70 da kafuwa

Shugaba Trump na Amurka ya zargi takwaransa na Faransa Emmanuel Macron da abin da ya kira kalaman batanci ga kungiyar Nato da cewa ''kwakwalwarsu ta mutu.''

Shugaba Trump dai na birnin Landan don halartar bikin cika shekara 70 da kafuwar kungiyar kawancen tsaro ta Nato.

Mista Trump ya ce Nato ta taka rawar gani, kuma kalaman Macron na cin mutunci ne.

Ya kara da cewa ya fara hasashen Faransa za ta fice daga kawancen, amma bai fadi dalilin da ya sa ya ce hakan ba.

Yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Mista Macron, Shugaba Trump ya yi amfani da tattausan harshe tare da cewa kasashen biyu sun yi abubuwan alheri masu tarin yawa tsakaninsu a matsayin abokan hulda.

Mista Macron ya ce ya san kalamansa kan kungiyar Nato sun zo da ban mamaki da kaduwa, "to amma yana nan kan bakansa."

Me ya janyo rarrabuwar kawuna a kungiyar?

Kasashen arewacin Amurka sun shiga kawancen Nato bayan kammala Yakin Duniya na Biyu, don magance barazanar mamayar Tarayyar Soviet.

Kasashe 29 mambobin kungiyar sun yi alkawarin tsayawa tsayin daka don kare junansu daga duk wata barazana.

Sai dai kalaman da Shugaba Macron ya yi a watan da ya gabata kan cewa mambobin ba za sa ayyuka kamar yadda ya kamata ya tada kura.

Macron ya kira kawancen da wadanda suka samu mutuwar kwakwalwa.

Da kuma zargin Amurka da kin tuntubar Nato kafin janye dakarunta daga arewacin Syria.

Me Shugaba Trump ya ce?

A ranar Talata a wajen taron manema labarai tare da sakatare janar na kungiyar Nato Jens Stoltenberg, Shugaba Trump ya ce Nato ta yi rawar gani kan ayyukan da aka kafa ta dominsu.

Da aka tambaye shi mai zai ce kan kalaman Mista Macron, sai ya ce daman shugaban Faransar ba ya girmama sauran mambobin kungiyar Nato.

Daga nan ya kara da cewa "Kalaman nasa tsagwaron rashin kunya da raini ne, da ma cin mutunci. Kuma ina ganin Faransa tana da tarin marasa ayyukan yi, tattalin arzikin kasar ba ya samun ci gaba.''

''Kalamansa ba su dace ba sam, alhalin kuna cikin wani yanayi da kuke bukatar tsamo tattalin arzikin kasarku, baki dayan shekarar nan ba ta musu armashi ba."

"Don haka bai kamata ka dinga maganganu irin haka kan kungiyar Nato ba. Wannan rashin da'a ne,'' in ji shugaba Trump.