Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi Ganduje kan sabbin masarautu

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bayanin Dahiru Bauchi kan rokon Ganduje ya soke sabbin masarautu

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren Bayanin Dahiru Bauchi kan rokon Ganduje ya soke sabbin masarautu

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheikh Dahiru Bauchi ya roki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje cewa ya janye aniyyarsa ta dawo da sabbin masarautun jihar.

Malamin ya bayyana hakan ne a wani sakon murya da ya aiko wa BBC Hausa.

A cikin sakon malamin ya ce: ''Ina rokon Ganduje don Allah, don Annabi ya bar batun (kirkiro da sabbin masarautu) kamar yadda kotu ta soke su.''

Ko a kwanakin baya sai da malamin ya nuna rashin jin dadinsa bayan an kafa masarautun..

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce "ina jawo hankalinsa ya janye maganar nan, yadda kotu ta rushe wadannan abubuwa nasa, to ya hakura tun da (kotu ta mayar) da Kano kamar yadda take shekara dubu da wani abu.''

Malamin ya ce "Ganduje ya kammala aikinsa cikin zaman lafiya, ya fi kan ya kammala ana tsine masa.''

Ya kuma ce ''taba fadar Kano, taba mu ne gaba daya 'yan Tijjaniyya da masoyanmu.''

Malamin dai ya ce da fatan gwamnan za ta ji shawarar da ya ba shi kuma ya bar Kano ta zauna lafiya kamar yadda ya same ta.

A ranar Litinin ne Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aika da wani sabon kudiri ga majalisar jihar, domin kafa sabbin masarautu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.

An fara wallafa labarin ranar 3 ga watan Disamba

Labarai masu alaka