Tsoffin gwamnoni sun cancanci a ba su fansho – Sule Lamido

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar Sule Lamido da BBC kan fansho

Tsohon gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya Sule Lamido ya ce tsofaffin gwamnoni sun cancanta a ba su fansho duba da cewa ana bai wa masu rike da mukaman gwamnati da dama bayan sun sauka.

A wata hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa, Sule Lamido ya ce hikimar yin dokar bai wa tsofaffin gwamnonin fansho ita ce saboda su yi aiki tukuru tsakani da Allah a lokacin da suke kan mukamansu.

A kwanakin baya ne batun bai wa tsofaffin gwamnoni fansho ta tayar da kura a Najeriya a lokacin da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya aike wa Gwamna Matawalle wasika cewar yana a biya shi fanshinsa har na naira miliyan 10 da ya kamata a ba shi duk wata.

Batun ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a kasar inda wasu da dama suke ganin tsofaffin gwamnonin ba su cancanci kudin fansho ba komai kankantarsa.

Amma tuni Gwana Matawalle ya bukaci majalisar jihar Zamfara ta soke dokar bayan ce-ce-ku-ce.

A makon da ya gabata ma tsohon gwamnan jihar Kaduna a jamhuriya ta biyu Alhaji Balarabe Musa ya ce shi naira dubu 700 ake ba shi a matsayin fansho.

Sule Lamido wanda ya ce ana ba shi naira 667,000 a matsayin fansho ya ce "Idan kuma ba a gamsu gwamnoni ba sa aiki tsakani da Allah ba to gara a soke dokokin da suka shardanta ba su fanshon.

"Amma ai ana bai wa tsofaffin manyan sojoji da manyan alkalai da shugabannin gidan yari da na hukumar shige da fice da sauran su, to shi ma gwamna ai aiki ya yi wa gwamnati," in ji tsohon gwamnan jihar Jigawan.

Hakkin mallakar hoto Sule Lamido Facebook
Image caption Idan kuma ba a gamsu gwamnoni ba sa aiki tsakani da Allah ba to gara a soke dokokin da suka shardanta ba su fanshon

Sule Lamido ya kuma ce kowace jiha na sanya fansho ne daidai da arzikinta da yawan kudin da gwamnatin tarayya take ba ta, "watakila Zamfara na cikin wadannan jihohin masu dumbin arziki shi ya sa ake bai wa tsoffin gwamnoni miliyan 10.

"Amma dai duk da haka miliyan 10 ta yi yawa," in ji shi.

'Ba a bani sauran abubuwa'

Sule Lamido ya kuma ce a dokar tsofaffain gwamnonin akwai batun bai wa gwamna da mataimakinsa da shugaban majalisa da mataimakinsa gidaje da motoci biyu duk bayan shekara hudu, da daukar nauyin asibiti a Najeriya ko a kasar waje, ba ya ga kudi daidai albashin gwamna mai ci.

"Daga cikin wadannan fansho na kudi kawai ake ba ni duk wata amma sauran abubuwa ba a taba ba ni ba. Kuma na tabbata ba ni kadai ne ba a bai wa ba don akwai Ali Sa'adu akwai Saminu Turaki amma su ma na san ba a ba su komai baya ga kudin fansho.

"Babu amfani zuwa ka tuna wa gwamna mai ci, idan hamayya ta sa ba ya bayarwa ai shi ma zai sauka wata rana."

Tsohon gwamnan ya ce idan dai har halin talauci da ake ciki a kasar ne ya sa ba a ba su sauran abubuwan da doka ta yarda, "to abu ne mai kyau, idan dai har za a yi amfani da kudin a yi wasu ayyukan. Muna murna da hakan."

Mene ne fansho?

Fansho na nufin wani tanadi da ake yi wa ma'aikaci lokacin da ya ke bakin aiki domin cin gajiya a gaba bayan barin aiki da manufar kange shi daga taba dukiyar baitil mali.

Kwamared Kabiru Dakata, CITAD

Dokar fansho ta Najeriya ta 2004 wadda aka yi wa gyaran fuska a 2014 ta tanadi:

Ma'aikaci zai bayar da akalla kaso 10 na albashinsa

Gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu za su bayar da akalla kaso takwas kan abin da ma'aikacinsu ya biya.

Sai dai dokar ta kara da cewa akwai damar sake yin waiwaye ga yawan kudin ma'aikatan lokaci zuwa lokaci.

Labarai masu alaka