Pochettino na jiran a sallami Solskaer, VAR na da matsala

Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tottenham ta ce a shirya take ta karbi kasa da fam miliyan 40 ga dan wasan tsakiyarta Christian Eriksen mai shekaru 27. (Evening Standard)

A wata mai kama da haka kuma, tsohon mai horar da 'yan wasan Tottenham din Mauricio Pochettino na son maye gurbin Ole Gunner Soskjaer a Manchester United. (Manchester Evening News)

Rahotanni sun ce Jose Mourinho ya dakatar da neman dan wasan tsakiyar kungiyar Sporting Lisbon ta Portugal Bruno Farnandez saboda kudin warware yarjejeniyarsa da suka kai fam miliyan 85. (Mail)

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai ya ce na'urar VAR da ke tantance abin da ya faru lokacin wasa na da matsalar da ba za a iya gyaranta ba. (Mirror)

Arsenal ta shigar da mai horar da 'yan wasan Valencia Marcelino a jerin wadanda take tunanin dauka. (Goal - a Spaniyanci)

Mai horar da Manchester United Soskjaer ya ce yana so kungiyar ta yi gaggawar shiga kasuwa neman 'yan wasa bayan ya bulguta cewa mataimakin mai tafiyar da kungiyar ya yi lattin yin hakan a bara. (Evening Standard)

Mai horar da 'yan wasan Manchester City Pep Guardiola ya ce babu batun sayen wani dan wasa a kungiyar a watan Janairu duk da matsalar masu tsaron baya da yake fuskanta. (Independent)

Norwich da Watford da kuma Crystal Palace na sa ido kan matashin dan wasan kungiyar Enfield Muhammad Faal mai shekara 22, wanda dan uwa ne ga mai tsaron bayan Liverpool Joe Gomez. (Sun)

Labarai masu alaka