'Yadda malariya ta kashe min 'yata mai shekara 18'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da uwar da maleriya ta kashe mata budurwar 'ya

Latsa alamar lasifika don sauraren hirar da Aisha Shariff Baffa ta yi da mahaifiyar yarinya

Wata mahaifiya da ta rasa 'yarta mai shekara 18 da dalilin zazzabin maleriya ta bayyana irin wahalar da 'yar ta shiga kafin kwananta ya kare.

Matar ta bayyana cewa zazzabi ne mai zafi ya rufe yarinyar da ya kai har jinin jikinta ya janye kuma sai da aka kara mata ruwa.

Sannan ta ce ko da suka je asibiti, an dauki lokaci mai tsawo kafin ma'aikatan lafiyar su bai wa 'yarta kulawar da ta dace.

"Da farko da muka je saboda tsananin cikowar asibitin mun wahala kafin mu ga likita sannan kuma suka ce mana babu gadon da za a kwantar da ita. Sai da muka rika roko sannan suka ba ta taimakon gaggawa," in ji mahaifiyar.

"A zaune a kan wani benci aka sa mata ruwa, babanta na tsaye ya rike ta don ko a lokacinma kanta ya fara langabewa, kafin daga bisani muka samu gado da kyar."

"Sai da wata mata ta mutu shi ne muka roka aka dauke gawar sannan aka ba mu gadonta" a cewarta.

Mahaifiyar ta ce a gida aka fara ba ta kulawa don a gida ma aka fara sa mata ruwan kafin daga baya su je asibiti.

A asibiti kuma an yi mata karin jini bayan da aka fahimci cewa jinin jikinta ya ja baya amma saboda illar da cutar ta yi a jikinta, ta rasu a asibitin.

Mahaifiyar ta bayyana cewa ta kadu matuka da rasuwar 'yarta saboda yarinya ce mai ladabi da hangen nesa kuma mai son taimako.

Ta ce "Ta kan ce min, mama in shaa Allahu sai na yi karatu ko don nan gaba ki huta."

Zazzabin maleriya dai na daya daga cikin manyan cututtukan da ke saurin kisa musamman a kasashe masu tasowa kuma wadnda da ke yanki mai zafi.

Wadannan yankuna na fama da rashin asibitoci masu kyau ko kwararrun likitoci ko kuma kayan aiki, don haka ba a bayar da kulawar da ta dace.

Wani lokaci kuma a kan yi tsaikon zuwa asibiti ko kuma a sayi magunguna a shagunan siyar da magunguna ba tare da an san takamaimai tsananin cutar ba.

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa Najeriya ce kan gaba da kashi 25 cikin 100 na yawan maleriya.

Alamomin cutar maleriya

  • Zazzabi mai zafi
  • Ciwon kai
  • Jin sanyi
  • Amai
  • Ciwon ciki/gudawa
  • Tashin zuciya
  • Rashin jin dadin jiki gaba daya

Labarai masu alaka