EFCC ta gurfanar da 'Mama Boko Haram' a gaban kotu

Ibrahim Magu Hakkin mallakar hoto Others

Hukumar yaki da cin hanci a Najeriya EFCC ta gurfanar daTahiru Saidu Daura da Barista Aisha Alkali Wakil, wadda ake yi wa lakabi da Mama Boko Haram, a gaban kotu bisa zargin laifin zambar kudi naira miliyan 66.

Hukumar ta ce mai Shari'a Aisha Kumaliya ce ta babbar kotun jihar Borno za ta jagoranci shari'ar a yau Laraba, inda ake zarginsu da laifuka har uku.

Mamallakin kamfanin AMTMAT Global Ventures mai suna Ali Tijjani ne ya yi korafi kan gidauniyar Complete Care and Aids Foundation, wadda Mama Boko haram ke jagoranta, bisa zargin zamba kan biski da ya samar wa gidauniyar.

Sai dai jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa tuni kotun ta yi zaman kuma har an bayar da belin Aisha Alkali Wakili kan kudi naira milyan 30, amma saboda rashin halartar wadanda ake zargin kotun ta ce za ta dage bayar da belin.

Wadanda ake zargin ba su amsa laifin da ake zarginsu da shi ba, kuma mai shigar da kara, fatsuma Muhammad ta bukaci kotu ta sa ranar sauraren shari'ar sannan ta bukaci a tsare su a gidan kaso har sai an kammala shari'ar.

Mai Shari'a Kumaliya ta bayar da beli kan naira miliyan 30.

Barista Aisha Alkali Wakil ta taka rawa yayin tattaunawar sulhu tsakanin kungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya, abin da ya sa ake yi mata lakabi da 'Mama Boko Haram'.