An samu gagarumar hujja don tsige Trump

US President Donald Trump. Photo: 3 December 2019 Hakkin mallakar hoto Reuters

Hujjojin da aka samun domin tsige shugaban Amurka Donald saboda laifin keta hurumin ofishinsa na da "karfi sosai", in ji kwamitin da ke jagorantar binciken tsige shugaban.

Shugaban kasar ya fifita biyan bukatunsa na siyasa "a kan muradun kasar Amurka, a cewar wani muhimmin rohoton da kwamitin ya gabatar wa majalisar dokokin kasar.

Rahoton ya ce "shugaban ya yi hakan ne ta hanyar "neman katsalandan daga kasashen waje" musamman Ukraine a kokarinsa na neman karin wa'adi a zaben shekarar 2020 mai kamawa.

An shirya rahoton ne domin tabbatar da hujjojin da za su bayar da damar a tsige Trump.

Sai dai shugaban ya musanta aikata zargin da ake masa na aikata ba dai-dai ba. Ya kuma bayyana binciken a matsayin bi-ta da kulli.

Tun gabanin fitowar daftarin rahoton, shugaban dan jami'iyyar Republican ya soki lamirin binciken da 'yan Democrat ke jagoranta a matsayin "tsananin rashin kishin kasa".

Bayan wallafa rahoton, Sakataren yada labaran fadar White House, Stephanie Grisham, ya ce 'yan jam'iyyar Democrat "sun gaza wajen kafa hujjar samun Trump da laifi", kuma rahoton nasu ba komai ba ne face "alamar irin tashin hankalin da 'yan Democrat ke ciki".

Yanzu za a mika wa Kwamitin Shari'a na majalisar dokokin kasar, wanda a ranar Larabar nan zai fara mahawara a kan rahoton da kuma yiwuwar tsige Trump din saboda zargin.

Me rahoton ya ce?

A ranar Talata ne Kwamintin binciken sirri na Majalisar dokokin Amurka ya fitar da rahoton binciken tsige Trump saboda badakalar Ukraine.

Kwamitin ya ce rahooton ya "bankado kokarin da Shugaba Trump ya shafe watanni yana yi na yi wa tsaron kasarmu zagon kasa domin biyan bukatun wasu bincike biyu da ake gudanarwa domin cimma manufar siyasa, da za ta taimaka masa a yakin neman sake zabensa.

"Shugaban ya kuma bukaci zababben shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya sanar a bainar jama'a cewa suna gudanar da bincike a kan Joe Biden, wanda shi ne babban abokin hamayyan da Trump din ya fi shakka a zaben da ke tafe.

Trump ya kuma nemi Zelensky da ya wofintar da maganganun da ake yi cewa Ukraine ce, ba Rasha ba ta yi katsalandan a zaben shugaban Amurka a 2016.

Rahoton ya ce ya samu kwararron hujjoji fiye da kima cewa Trump ya saba ka'idar aikinsa kuma ya kawo wa majalisar kasar tarnaki.

Sautin waya ya kara wasu hujjojin

Duk wanda ya saurari Adam Schiff da irin jawabinsa na karshe makonni biyu da suka gabata a wajen sauraren bahasi kan batun tsige Shugaba Trump zai yi mamakin sakamakon binciken da aka gabatar a ranar Talata.

Kundin mai shafi 300 na dauke da sabbin bayanai.

Kamfanin sadarwa na AT&T ya bai wa kwamitin binciken abin da suka nada daga wayar tarhon Rudy Giuliani, sannan wannan ya sake bayyana lokacin da lauyan Shugaba Trump ya tattaunawa da Fadar White.

Binciken wayar tarhon an fara shi daga watan Afirilun shekarar nan, inda lauya Giuliani ya kira wasu jerin lambobin tarho na fadar White House, musamman ofishin kasafin kudi, da ofishin da ke kula da tallafin sojin Amurka ga Ukraine.

Bayyanar wadannan sabbin bayanan da ba a san da su ba, sun nuna yadda lauyan Shugaba Trump ke aiki gaba gadi tare da manyan jami'an gwamnati.

Shaidu kamar tsohuwar jakadar Amurka a Tarayyar Turai Gordan Sondland, ta ba da shaidar yadda Mista Giuliani ke ba su umarni kai tsaye kuma daga shugaban kasa, kan su matsa wa jami'an Ukraine lambar fara binciken da zai bai wa Shugaba Trump fifiko ta fuskar siyasa.

Me zai faru?

Kwamitin na binciken sirrin ya kada kuri'a a ranar Talata, inda mutum 13 suka amince a tabbatar da rahoton bincken tare da mika shi ga kwamitin shari'a na majalisar wakilan Amurka, yayin da tara ba su amince ba.

Kwamitin binciken shari'ar zai yi zama na musamman tare da kwararrun da za su yi bayani dalla-dalla kan tsarin da ake bi wajen tsige shugaba.

Fadar White ta ki yarda a yi zaman da ita, wanda ta ce babu adalci sam a ciki.

Wasu daga abubuwan da za a duba kan batun tsigewar shi ne amfani da karfin iko ba bisa ka'ida ba, da hana shari'a aikinta ta hanyar amfani da majalisa.

'Yan jam'iyyar Democrat dai suna son kada kuri'a kan batun tsigewar a majalisar wakilai kafin karshen shekarar nan, yayin da ake ganin majalisar dokoki ka iya yin hakan a watan Junairun badi.

Me 'yan Republican ke cewa?

Kafin a bayyana sakamakon binciken a bainar jama'a, jam'iyyar Republican ta wallafa nata rahoton mai shafi 123, wanda ya yi Allah-wadai kan shaidar da wani ya ba da na cewa bai amince da tsarin Shugaba Trump kan yadda yake kallon duniya.

Haka kuma rahoton ya zargi jam'iyyar Democrat da kokarin kaucewa muradun Amurkawa, tare da zargin tun ranar da shugaban ya kama aiki suke kokarin tsige shi daga mukaminsa.

"Duk cikin shaidun da Democrat ta gayyato babu wanda ya ba da shaidar ba da rashawa, ko wawure dukiya ko wani babban laifi,'' haka kuma duk cikin abubuwan da ake magana akai babu inda ya aminta a tsige shugaba matukar ba a same shi da laifi ba.

Tuni Adam Schiff ya yi watsi da rahoton na Republican, inda ya ce suna kokarin kaucewa shaidun da aka samu ne da gangan.

A bangare guda Shugaba Trump ya caccaki Mista Schiff a wajen taron bikin cika shekara 70 da kafuwar kungiyar kawancen tsaro ta Nato da ake yi a birnin Landan, inda ya kira shi "mutumin da bai san abin da yake yi ba."

Me ake zargin Trump da aikatawa?

'Yan jam'iyyar Republican sun ce shugaban ya kwadaitawa Ukraine abubuwa guda biyu, na farko tallafin soji da ya kai dala miliyan 400, wanda tuni majalisar Amurka ta ware.

Sai kuma ganawa da Mista Zalensky a fadar White House don ya sa a gudanar da binciken. 'Yan majalisar sun kara da cewa wannan matsin lamba da shugaban ya sanyawa daya daga cikin aminan Amurka masu rauni ya saba wa doka.

Binciken farko da Mista Trump yake son Ukraine ta yi kan Mista Biden ne babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar Democrat, da dansa Hunter, wanda yake cikin shugabannin kamfanin makamashi na Ukraine a lokacin da mahaifinsa yake mataimakin shugaban kasa.

Abu na biyu da Shugaba Trump ya bukata shi ne Ukraine ta shirya wata makarkashiya kan cewa Rasha ba ta yi kutse a zaben shugaban Amurka ba, wanda hukumomin leken asiri na Amurka da suka bukaci a sakaya sunansu suka ce alamu sun nuna karara Rasha ta yi kutse a sakonnin email na jam'iyyar Democrat a shekarar 2016.

Yaya ake tsige shugaba a Amurka?

Tsigewar ita ce bangare na farko - sai tuhume-tuhume - inda 'yan majalisar dokoki za su iya tsige shugaba daga mukaminsa.

Daga nan, bayan sauraron batun majalisar wakilai za ta ka da kuri'ar tsige shi, hakan zai tilasta wa majalisar dattawa ta yi zama kan batun.

Ana bukatar rinjaye kaso biyu-bisa uku kafin a samu shugaban da laifi kuma a tsige shi - amma hakan na da wuya ya faru a wannan karo saboda yadda jam'iyyar Shugaba Trump take da rinjaye a majalisar dattawa.

Shugabannin Amurka biyu ne kawai aka taba tsigewa (Bill Clinton da kuma Andrew Johnson) a tarihin Amurka, amma babu wanda aka samu da laifi a karshe.

Shugaba Richard Nixon ya yi murabus ne kafin a kai ga tsige shi.

Labarai masu alaka