Ba mu kwace filin Sarki Sanusi ba – Gwamnatin Kano

Sarki Muhammadu Sanusi II Hakkin mallakar hoto fadarkanotadabo
Image caption Gwamnatin Kano da fadar masararutar kano na takun saka

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa ta kwace wani fili mallakar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II saboda aikin hanyar karkashin kasa da take yi a shataletalen Dangi da ke kan titin Zaria.

A makon da ya gabata ne wasu jaridu a Najeriya suka ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta karbe filin domin yin aikin hanyar karkashin kasa, wanda aka kimanta kan naira miliyan 250, inda gwamnatin ta biya shi miliyan 4.5 kacal.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kula da filaye ta jihar Murtala Shehu Umar ya fitar, ya ce gwamnati ba ta karbi wani fili daga basararken ba duk da cewa gaskiya ne aikin ya shafi wani bangare na filin nasa.

"Daga cikin wuraren da rusau ya shafa akwai katangar filin guda biyu, daya tana kan titin Ibrahim Dabo inda dayar take kan titin Dr Borodo," in ji sanarwar. "Kuma da sanin Mai Martaba aka rushe su."

Sanarwar ta ci gaba dacewa: "A saboda haka ne wannan hukuma take kira ga Mai Martaba da ya bijiro da bayan asusunsa na banki domin karbar diyyarsa bisa umarnin da gwamnati ta bayar na biyansa da kuma sauran wadanda abin ya shafa.

"Sai dai har yanzu Mai Martaba bai kai ga turo da bayanan asusun bankin nasa ba."

Sanarwar ta kara da cewa ba duka filin abin ya shafa ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka yi ikirari.

Masarautar karkashin Sarki Sanusi na takun saka da gwamnatin jihar Kano, abin da ya sa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar.

A wannan makon ne ake sa ran majalisar dokokin jihar za ta yi muhawara kan sabon kudirin dokar kirkiro masararutn biyto bayan hukuncin kotu da ya soke wanda ta yi a baya.

Labarai masu alaka