Budurwa ta mutu a kokarin ceto wani mutum a ruwa

Anna Nduku
Image caption Ruwa ya tafi da matashiya Anna Nduku, a lokacin da ta kubutar da wani mutum

Masu aikin ceto a kasar Kenya, sun gano gawar wata matashiya da ruwa ya tafi da ita a lokacin da take kokarin ceto wani mutum da ya makale yayin da yake kokarin ketara wani kogi.

A ranar Talata ne matashiyar mai suna Anna Nduku, 'yar shekara 19 ta fada kogin Kandisi wanda ke kusa da Ongata Rongai, a wajen birnin Nairobi.

Tana daya daga cikin fiye da mutum 130 da suka mutu sakamakon ambaliyar da mamakon ruwan sama da ake ta shekawa tun cikin watan Oktoba.

Nduku dai ta je don kubutar da wani mutum da yake ta sheka ihun neman taimako, sakamakon ballewar da gadar da ba a kammala ta ba ta yi.

Mutumin ya tsira da ranshi, bayan Nduku ta fada cikin ruwan a lokacin da ta kubutar da shi.

Mahaifiyar Nduku Misis Elizabeth Mutuku tana kusa da wurin da abin ya faru ta ce ''Ina kallon lokacin da take kokarin fitowa daga ruwan, ni ma na yi kokarin kubutar da ita. Ina ta kiran sunanta Anna, Anna, amma lamarin ya fi karfina.''

''Na so jefa ma ta sanda, idan ta kama zan iya janyo ta waje. Amma ruwan kogin yana da karfin gaske, haka ya yi ta gungura ta daga wannan wuri zuwa wancan, kafin daga bisani ruwan ya tafi da ita," in ji mahaifiyar Anna.

Kogin dai ya cika makil, kuma tun ranar Litinin ake sheka ruwa kamar da bakin kwarya, wanda wani bangare ne na mamakon ruwan da yankin gabashin Afirka ya fuskanta da aka shafe sama da makonni hudu ana yi.

Labarai masu alaka