Shin Rahama Sadau ta sauya sana'a ne?

Rahama Sadau Hakkin mallakar hoto TWITTER/RAHAMA SADAU

Jarumar fina-finan Kannywood da Nollywood Rahama Sadau, ta raba kafa inda ta bude wani wajen ciye-ciye da shaye-shaye a Kaduna mai suna Sadauz's lounge.

Jarumar wadda fitacciya ce a cikin fina-finan Hausa na kannywood, ta bude wajen ne musamman domin matasa.

Ana gudanar da abubuwa da dama a wajen, kamar gasa nama da kifi da kuma shan lemuna da shisha.

Kazalika akwai kuma wajen gyaran gashin mata da na maza da wajen kwalliya da kuma wasanni kala-kala domin nishadi.

A shafinta na twitter, Rahama Sadau ta wallafa wasu daga cikin hotunan bude wajen, inda ta gayyaci 'yan uwa da abokan arziki domin su ta ya ta murna.

An ci an sha a wannan waje.

Sharhi, Aisha Shariff Baffa

Jama'a na ganin cewa kamar Rahama Sadau ta raba kafa ne shi ya sa ta bude wannan waje, kasancewa ba kasafai ta ke fitowa a fina-finai ba a yanzu.

A shekarun baya, tauraruwar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta sha suka musamman a kafofin sada zumunta sakamakon rungumar mawakin nan, Classiq da ta yi.

Wannan ya jawo suka matuka ga Rahama Sadau da Kannywood baki daya, inda akasarin jama'a ke nuna cewa abin da ta yi ya saba wa addininta da kuma al'adar Bahaushe.

Wannan ne ya ja har hukumar da ke sa ido kan tace fina-finai ta dakatar da ita duk da cewa wasu sun yi korafi kan cewa wasu 'yan wasan sun yi abin da ya fi na Rahama, kuma ba a dauki mataki a kansu ba.

Hakkin mallakar hoto TWITTER/RAHAMA SADAU

Labarai masu alaka