Yakin Syria: Hare-haren sama sun kashe mutum 24 a Idlib

A Syrian woman walks past buildings destroyed in a reported government air strike in the town of Maasaran in Idlib province, 17 December 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin yakin gwamnatin Syria ya kai hari garin Maasaran

An kashe fararen hula 24 a wasu hare-haren sama da aka kai yankin Idlib da ke karkashin ikon 'yan tawaye a Syria.

Kungiyar bayar da agaji ta White Helmets ta ce mutum tara da suka hada da yara uku sun mutu a yayin da jiragen yaki suka jefa bama-bamai garin Talmenes.

A hannu guda kuma mata da 'ya'yan wani dan kungiyar agajin uku na daga cikin 'yan gida daya shida da suka mutu a lokacin da aka yi luguden wuta a kauyen Badama.

Rahotanni sun ce wani harin sama da aka kai garin Maasaran ya kashe mutum shida.

Idlib ne waje na karshe da har yanzu yake karkashin ikon 'yan tawaye da masu ikirarin jihadi da ke adawa da Shugaba Bashar al-Assad.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa yankin waje ne mai al'umma miliyan uku da suka hada da yara miliyan daya.

Fiye da kashi 40 cikin 100 na wajen sun fito ne daga yankunan da a baya suke karkashin ikon 'yan tawaye.

Wata sasantawar tsagaita wuta da Rasha ta jagoranta ta taimaka wajen dakatar da kai hare-haren gwamnati a Idlib a watan Agusta.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da kai hare-hare kusan kullum a yankin.

A ranar 7 ga watan Disamba hare-haren sama da aka kai yankin da ke karkashin ikon 'yan tawaye sun kashe mutum 20.

Mutum tara daga cikin wadanda suka mutu din 'yan kauyen Balyoun ne inda aka kai harin a kasuwar garin.

Labarai masu alaka