'Mutanen da ba sa cin nama ba su cika narka kiba ba'

Abincin da babu nama a ciki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Abincin da babu nama a ciki

Kwararru sun gargadi mutanen da ba sa cin duk wani nau'in nama su tabbatar suna cin abin da zai ba su isasshen vitamin B12, saboda hadarin samun tawayar lafiyarsu.

Sun bayyana hakan ne gabanin taron shekara-shekara da ake yi a watan Junairu da mutanen da ba sa cin nama ke shiryawa.

Nau'in abincin da wadannan mutane ke ci na dauke ne da harza da rashin maiko yayin da wasu daga cikin abincin ke janyo raguwar vitamin B12.

Kungiyar mai suna Vegan Society, ta ce suna samun nau'in vitamin din cikin abincin da suke ci ko da kuwa ba wadataccen ba ne.

A kowacce rana ana bukatar 'yan shekara 15 zuwa sama su ci akalla 1.5 nau'in abincin dai zai kara musu vitamin B12.

Ana samun hakan a cikin jan nama da kifi da kwai da madara. Amma ba a samun su a cikin abinci dangin hatsi da kayan marmari ko kayan lambu ko shan magani.

Tawayar da vitamin B12 ke haddasawa a jikin dan adam suna da yawa, ciki har da kassara jijiyar da ke kai jini kwakwalwa da bargon dan adam.

Har wa yau, suna daukar shekaru hudu ko sama da haka kafin su fara nuna alamu a hannu da kafa.

'Za a iya kaucewa hakan'

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Farfesa Tim Key, shi ne mukaddashin daraktan sashen nazarin cutar daji a jami'ar Oxford ya ce: "Ba za ka samu tawaya ba don ba ka cin abincin da babu vitamin B12 a ciki."

To amma farfesa Tim wanda shi kansa ba ya cin abinci dangin nama da kuma ya ke shan kwayar maganin vitamin B12 ya kara da cewa: "Idan mutane su ka zabi rayuwa ba tare da cin dangin nama ba abin ba zai dame ni ba, to amma fa zan damu matuka idan ba su san cewa suna bukatar vitamin B12 ba,''

Masana kimiyya sun ce tallace-tallacen da ake yi a shafukan internet kan cewa marasa cin nama ba sa bukatar karin vitamin B12, ya danganta ga bayanan da suka samu a wajen mutane daban-daban.

Shi ma farfesa Tom Sanders, kwararre kan nau'in abinci mai gina jiki a kwalejin King da ke London, ya ce: "Duk cikin nau'oin sinadarin vitamin da jikin dan adam ke bukata, babu kamar B12 don tasirinsa ya fi sauran.

Na damu matuka kan mutanen va ba su d isasshensa musamman batun tawaya.''

Ya kuma yi karin haske kan wata mace da ke shayarwa, kuma ba ta da isasshen vitamin B12 ga kuma tawayar da ta samu hakan ya shafi jaririn da shi ma ya samu matsala sosai.

"Abu ne mai sauki a kauce wa faruwarsa, abin da ya fi damu na yadda ake samun karuwar mutanen da ba sa cin nama wadanda ba su san illar da rashin vitamin B12 ke yi ga jikin dan adam ba, kuma ba su san suna matukar bukatar shi ba.''

'Tsarin abinci mai gina jiki'

Ba a cika kayyade illar da rashin cin nama ke haifar wa mutanen da ba sa ci ba, Amurka da Birtaniya sun yi nazari a kan mutane 10,000.

Kawo yanzu an gano mutanen da ba sa cin nama ba su cika narka kiba ba, sannan ba su da hadarin kamuwa da ciwon siga nau'i na biyu da ciwon zuciya.

Sai dai suna cikin hadarin yawan karyewar kashi, yayin da bincike na baya-bayan nan ya nuna suna cikin hadarin samun ciwon shanyewar barin jiki.