An kai hari a hedikwatar tsaron Rasha

Motocin 'yan sanda a Moscow sun tare layin shiga hedikwatar tsaron

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Motocin 'yan sanda a Moscow sun tare layin shiga hedikwatar tsaron

Wani mahari ya bude wuta a hedikwatar tsaro ta Rasha a birnin Moscow.

Harin na zuwa ne jim kadan bayan Shugaba Vladimir Putin ya kammala taron manema labarai na shekara-shekara.

Dan bindigar ya yi ta harbi da makami mai sarrafa kansa a kofar shiga ofishin, in ji shaidun gani da ido.

Jami'an tsaro sun yi wa yankin kawanya inda suka mayar da mutane zuwa cikin gine-ginen wajen.

Rahotanni na cewa maharin ya kashe jami'an tsaro uku, amma hukumomi ba su tabbatar da hakan ba tukuna.

Wasu hotuna da aka wallafa a intanet sun nuna wasu dauke da makamai na fita daga ginin hedikwatar tsaron.

Dakaru na musamman sun isa wurin yayin da aka ga motocin daukar marasa lafiya guda biyar na barin wurin, in ji shaidu.

An kai hari ne a jajibirin ranar hukumomin tsaron kasar, kuma Shugaba Putin na gabatar da jawabi a wani taro mai alaka da ranar hutun, sanda lamarin ya faru.