Yaudarar ango: Matan da ake yi wa kaciya domin dawo da budurcinsu

Amarya da Ango na rawa a Sudan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Amarya da Ango na rawa a Sudan

A cikin jerin wasikun da 'yar jarida kuma 'yar Afirka, Zeinab Mohammed Salih ke aiko mana, ta yi nazari a kan karuwar yin kaciya ga mata a kasar Sudan.

Wasu daga cikin matan kasar Sudan, na zuwa a yi musu kaciya watanni kadan gabannin su yi aure domin ango ya ce sun kai budurcinsu.

Yawancin matan dai an yi musu kaciya tun suna kanana, abin da ake yi tsakanin shekara hudu zuwa 10.

A yawancin kasashen musulmai a kan dangana da yanke dan tsaka da leben farji, ana kuma yin wasu dinke-dinke da nufin tsuke bakin farji.

Ana yin wannan dinki ga matan da suka san da namiji gabannin aure.

Idan amarya ta bukaci yin wannan dinkin, to aikin ungozama ne ta yanke wani sashe na leben farji tare da hadewa da kuma dinke shi.

'Zama ya same ki'

"Aikin tiyata ne mai matukar ciwo, saboda lokacin da aka yi min sai gidansu wata kawata na je na yi kwanaki don ba na son mahaifiyata ta san na yi,'' in ji Maha, daya daga cikin matan da suka taba yin wannan tiyata da muka sakaya sunanta.

''Hmm idan za ki yi tsarki tamkar attaruhu don radadi, ga shi ba na iya tafiya.''

An yi wa Maha dinkin watanni biyu gabannin aurenta da wani tsoho da ya girme mata nesa ba kusa ba.

''Idan ban yi dinkin ba, ba zai taba amincewa da ni ba saboda na san da namiji kafin na yi aure.''

''Zai haramta min fita daga gida, kai hatta wayar salula sai ya hana ni amfani da ita,'' in ji Maha.

Maha daliba ce mai shekara 20 a jami'ar Sudan, kuma jihar da ta fito daga arewacin kasar ta haramta yi wa mata kaciya.

Nau'o'in kaciya:

Bayanan bidiyo,

Me ake nufi da kaciyar mata?

  • Nau'i na farko: Wanda ake cire baki dayan dan tsaka
  • Nau'i na biyu: Cire baki daya dan tsaka da labban farji
  • Nau'i na uku: Cire labban farji baki daya, da dinkewa da kuma tsuke farji
  • Nau'i na hudu: Ana yankewa da dinkewa har da kone wani bangare na farji
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce har ynzu ba a daina yi wa mata kaciya a Sudan ba, inda kashi - 87 cikin 100 na matan kasar tsakanin shekara 14 zuwa 49 an taba yi musu daya daga cikin nau'o'in kaciya.

Duk da cewa Maha tana aiki ne a birnin Khartoum, birnin da ba a haramta yi wa mata kaciya amma ta zabi zuwa wajen ungozoma don yi mata aikin dinkin.

Daman ta san ungozamar, wadda ta amince ta yi mata aiki kan fam 5,000 na kasar, kwatankwacin dalar Amurka 110.

'Ina yi mu su kaciya ne don ina bukatar kudi'

Yawanci dai bisa al'ada, mace ta san da namiji gabannin aure haramun ne, don haka wasu matan ke yin karamar tiyata don a dinke su da nufin yin kwaskwarima da za ta lullube fatar farji ta ciki da waje dan kar ango ya gane sun taba yin jima'i da wani.

Amma ''dinkin farji'' kamar yadda ake kiran sa, likitocin fida ne kadai su ke yin sa kuma ba sa fai ake yi ba a kasar Sudan, an kuma shaida min asibiti guda daya ne jal aka amince ya yi aikin tiyatar kuma matan aure ne kadai suke zuwa.

Dan haka matan da ke son yin dinkin farji gabannin aure, dole su je wajen ungozoma. Wasu daga ciki kan yanke labban farji ko wani bangare na dan tsaka.

Wata kwararriyar likitar mata Dr Sawsan kuma mai fafutukar ganin an daina yi wa mata kaciya ta ce;Duk wani abu da aka yanke a farjin mace sunansa kaciya, ko da kuwa an dinke.''.

Zeinab Mohammed Salih
Zeinab Mohammed Salih
At three hospitals I visited midwives were happy to offer me the various procedures"
Zeinab Mohammed Salih
Journalist

Harwayau duk abin nan da ake yi, babu abu guda da ake yi a asibiti a birnin Khartoum, saboda kungiyar likitocin Sudan ta haramta hakan.

Duk ungozomar da aka samu da yin kaciya, to korarta ake yi daga bakin aiki.

Amma duk da haka asibitoci uku da na kai ziyara, ungozoma uku sun shaida min hanyoyin da ake bi wajen yin aikin.

Daya daga cikinsu ta min bayanin komai a gaban sauran jami'an lafiya mata ta kuma nuna min dakin da ake yin wannan aiki.

''Ki na son na yanke wani bangare na dan tsakar? Idan ba kya son na taba wannan, ba zan miki ba... amma zan miki aiki mai kyau yadda za ki koma budurwa, ta hanyar dinke leben farjinki ta ciki da waje, in ji ta.

''Kwanakin baya na yi wa wata yarinya 'yar shekara 18 dinki, saboda dan uwanta ya yi mata fyade ta bude kwarai, mahaifiyarta ta zo tana kuka da rokon na taimaka mata asirinta ya rufu.''

''Na yi wa cibiyar Saleem alkawarin ba zan kara yi wa mata da 'yan mata kaciya ba, to amma lokaci zuwa lokaci ina yi saboda ina koyawa jikokina da mahaifiyarsu ta rasu yadda ake yin kaciyar, kudin da nake samu da shi nake biya musu kudin makaranta,'' in ji matar.

Shirin cibiyar Saleem dai Majalisar Dinkin Duniya ce ke daukar nauyinsa, kuma an kaddamar da shi a shekarar 2008 don magance matsalar yi wa 'ya'ya mata kaciya.

An bude sabon babi?

Za a dauki dogon lokaci kafin a magance matsalar, musamman ga mutanen da suka yi riko da al'adar.

Wani matashi a birnin Khartoum ya ce idan ya auri macen da ba ta kai budurcinta ba, ba zai taba amincewa da ita ba don kuwa ta ci amanarsa.

''Ina ma dai matar da zan aura za ta kasance sabuwa dal a leda, da na fi kowa farin ciki,'' in ji shi.

Wannan dai daya ce daga cikin dabi'ar mazan kasar Sudan, inda suke nuna maitarsu a fili ta son auren budurwar da ta kai bantenta.

Sai dai duk da haka, masu fafutuka na fatan wata rana a wayi gari an daina wannan dabi'a, musamman ganin a karon farko an samu zabar mace a matsayin minista da suke fatan ganin za ta kawo gagarumin sauyi, musamman ga 'yan mata da matan kasar Sudan.

Ko a watan da ya gabata gwamnatin kasar ta janye tsattsaurar dokar nan ta haramtawa mata sanya wando, da ake ganin sassauci ne ga matan Sudan.

An fara haramtawa mata sanya wando shekara 30 da suka gabata a zamanin mulkin Shugaba Omar Al-Basheer da aka hambarar da gwamnatinsa bayan zazzafar zanga-zanga a kasar.

Shugabar gidauniyar An Lan Iniciative Nahid Touba, mai fafutukar yaki da yi wa mata kaciya, ta ce 'yan matan yanzu sun waye fiye da iyayensu don haka ba lallai su amince da yi wa 'ya'yansu kaciya ba.