Donald Trump: Me tsige shugaban Amurka ke nufi?

Jajibirin ranar da Majalisar Wakilan Amurka za ta yi kuri'a a kan tsige Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar a birnin New York masu neman Majalisar Wakilan Amurka ta tsige Shugaba Trump

Donald Trump ya shiga jerin shugabannin Amurka da Majalisar Wakilan kasar ta tsige. Yanzu Trump ya zama shugaban Amurka na uku da majalisar ta tsige a tarihin kasar.

Majalisar ta samu Trump da aikata laifi biyu: Wuce hurumin ofishinsa da kuma kin bai wa majalisar hadin kai yayin gudanar da bincike.

Yaushe Majalisar Dattawan kasar za ta binciki zargin da ake wa Trump?

Majalisar dattawa ba ta fara komai ba tukuna. Amma ana ganin za ta fara nata binciken bayan 'yan majalisar sun dawo daga hutu a mako na biyun watan Janairu mai kamawa.

Abin da Chuck Schumer na jam'iyyar Democrat mara rinjaye a majalisar ya bayyana kenan.

Shugaban majalisar Mitch McConnell, daga jam'iyyar Republican ba zai so 'yan Democrat su nemi majalisar ta binciki Trump ba, amma zai iya yarda da wa'adin da bukatar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sadda Majalisar Wakilan Amurka ta fara zama a ranar tsige Donald Trump

Idan Majalisar Dattawa ta tsige Trump, wane tasiri abun da ya yi a wa'adinsa na farko zai yi a neman sake zabensa a 2020?

A yanzu ba za a iya fadin abin da zai faru ba.

'Yan Republican na ganin tsigewar za ta taimaka wa yakin neman sake zaben Trump domin magoya bayan shugaban na iya tausaya masa su mara masa baya.

Amma 'yan jam'iyyar Democrat na tunanin tsige Trump za ta yi masa mummunan tabon da masu zabe ba za su kawar da kai a kai ba a lokacin zabe.

Alkaluma sun nuna cewa ra'ayoyin 'yan Amurka sun bambata game da tsige shugaban. Har yanzu bata sauya zane ba, duba da dambarwar da ake cigaba da yi game tsige shugaban.

Asalin hoton, Getty Images

Idan Mike Pence ya zama shugaban kasar bayan tsige Trump, shin Pence zai iya nada Trump a matsayin mataimaki sannan ya sauka daga mukaminsa.

Za ta iya yiwuwa domin kundin tsarin mulkin kasar bai haramta hakan ba.

Amma kalubale na farko shi ne dole sai akasarin 'yan duka majalisun dokokin kasar sun amince da nadin da Pence ya yi wa Trump a matsayin mataimakinsa.

Da wuya hakan ta samu, duba da yadda Majalisar Wakilai wadda 'yan Democrat ke da rinjaye suka dage cewa sai an tsige Trump.

Idan kuma Majalisar Dattawan ta haramta wa Trump sake rike wani mukamin siyasa, to magana ta kare.

Amma idan ba ta yi haka ba, babu abin da zai hana Pence yin irin wannan sadaukarwar. Kuma Trump na iya sake neman takara a zaben 2020 har ma ya yi nasara.

Idan Majalisar dattawa ba za ta tsige Trump ba to ina fa'idar wannan bata lokaci?

Dalilin 'yan Democrat ke yin hakan shi ne suna ganin akwai nauyi a kansu na su tabbatar da cewa Trump ya girbi abin da ya shuka. Duk da cewa sun san da kyar Majalisar Dattawa ta tsige shi.

'Yan Democrat na ganin cewa Trump ya saba ka'ida wajen matsa wa Ukraine lamba ta fara bincike a kan abokin hamayyarsa.

Suna ganin idan har ba su taka masa burki ba - ko da ba'a tsige shi ba - to shugaban kasar zai samu kwarin gwiwar cigaba da yin haka, wadda ke iya yi wa jam'iyyarsu illa a zabe mai zuwa.

Bayan hakan akwai batun siyasa domin 'yan Democrat sun shafe watanni suna kira da a tsige Trump. Da ba su tsige shi a aikace ba, to da jam'iyyar ta rasa wasu magoya bayanta.

Hakan kuma na iya mata babban illa a zaben 2020 domin wasu magoya bayan jam'iyyar za su rasa kwarin gwiwar fita su kada kuri'a a zaben.

Asalin hoton, Alamy

Shin Trump zai iya sake tsayawa takara idan Majalisar Dattawa ta tsige shi amma ba ta kama shi da laifi ba? Wace illa hakan za ta yi masa?

Tabbas zai iya sake tsayawa takara. Tsigewa na iya masa illa a siyasance musamman yiwuwar ya sake cin zabe. Amma doka ba ta haramta masa sake tsayawa takara ba.

Kamar yadda aka fada a baya, ko da Majalisar Dattawa ta tsige Trump, zai iya cigaba da da yakin neman zaben da ya riga ya fara, matukar majalisar ba ta haramta masa rike mukamin siyasa ba.

Nawa aka kashe a kan wannan batu? Me 'yan Democrat suka yi wa 'yan Amurka a baya?

Da wuya a iya fadin yawan kudin da aka kashe. Amma an ware dala miliyan 23 domin binciken da Robert Mueller ya jagoranta kan katsalandan din Rasha a zaben Amurka. Amma binciken batun Ukraine kuma an gudanar da shi ne da kayan aiki da kuma ma'aikatan Majalisar Wakilan.

Maganar abin da ya fi muhimmanci kuma, wannan kuma fahimtar siyasa ita ce alkali.

Shugabancin Democrat ya yi daruruwan dokoki a Majalisar Wakilai. Kadan daga ciki su ne dokar daukar makamai da dokar karin albashi da dokar kare muhalli da daokar da dokar ba wa matata kariya. Sai dai kuma kadan daga cikin dokokin ne suka samu amincewar Majalisar Dattawa wadda 'yan Republican ke jagoranta.

A halin yanzu Majalisar Wakilan ba ta amince da kasafin shekarar 2020 ba, wanda aka fara aiki a kai tun a watan Oktoba.

Idan har zuwa tsakar daren ranar Juma'a majalisar ba ta amince da shi ba, to babu makawa sai gwamnatin kasar ta dakatar da ayyukanta a karo na biyu.

Dakatar da ayyukan gwamnati ya saba yin mummunan illa ga daidaikun mutane da kuma 'yan siyasa, kamar yadda 'yan kasar suka saba gani.

Wa ke jagorantar bincike kan tsige Trump, babban alkalin kasar ko 'yan Majalisar Dattawa?

Babban alkalin kasar shi ne doka ta ayyana a matsayin mai jagorantar binciken neman tsige shugaban kasa a zauren Majalisar Dattawa.

'Yan majalisar za su fara kada kuri'a kan fara binciken. Da zarar an fara to shugabancin zaman zai koma karkashin John Roberts har a kammala.

Sai dai kuma ko da babban alkalin ya yanke hukunci, 'yan majalisar na iya sokewa idan magoya bayan hakan sun fi rinjaye.

Saboda haka idan 'yan Republican suka ga dama za su iya soke hukuncin binciken da babban alkalin kasar ya yanke bayan zaman majalisar.

Ina adalci idan har aka tabbtar cewa Trump ya karya doka kasa amma Majalisar Dattawa mai rinjayen 'yan Republican ta ke tsige shi?

Wadanda suka tsara kundin mulkin Amurka a 1787 suna sane, amma suka mika ikon tsige shugabanni ga 'yan siyasa.

An tsara gwamnatin Amurka ne ta yadda za a samu daidaito tsakanin rassan gwamnati - bangaren zartaswa da majalisa da kuma bangaren sharia - da yiwuar sabani. An yi hakan ne domin kawar da danniya.

Don haka tsige shugaban kasa wani makami ne da majalisa ke da shi na kare ikonta da kuma gyara wa bangaren zartaswa zama.

Maganar adalcin hakan kuma abu ne ne mahawara.

Asalin hoton, Alamy

Shin jam'iyya ya kamata 'yan Majalisar Dattawa su bi ko adalci za su bi?

Zabin kowane dan majalisa yadda zai kada kuria'. 'Yan Republican irinsu Lindsey Graham, ya ce ya riga ya yanke wa kansa hukuncin kada kuri'ar wanke Trump daga laifin da ake zarginsa.

'Yan Democrat da yawa kuma sun bayyana karara cewa sun gamsu da hujjojin da aka gabatar wa Majalisar Wakilai na tsige Trump.

Su kadai suka san ko goyon bayan jami'yya ne ko gamsuwa da hujjoji suka bi wurin daukar matsayi kan tsige shugaban.

A karshe dai sai sun gamsar da masu zabe dalilinsu na daukar matakin, matukar za suk kara yin takara.

Abin da tsarin adalcin da dokar Amurka ta yi tanadi