An samar da hijabin dakin tiyata a Birtaniya

Ma'aikatan tiyata

Asalin hoton, University Hospitals of Derby and Burton

Bayanan hoto,

Karamar Farah Roslan ce a hagu tare da likitar fida Gill Tierney

Wani asibiti ya zamo na farko a Birtaniya da ya samar da hijabin da ake amfani da shi a dakin tiyata a kuma jefar idan an kammala amfani da shi, ga jami'an lafiyar da ke aiki a dakin fida.

Daya daga cikin kananan likitoci kuma musulma Farah Roslan ce ta kirkire shi a lokacin da take aikin gwaji a asibitin Royal Derby na Birtaniya.

Ta dauki matakin ne saboda tsoron daukar cuta da ka iya makalewa a jikin hijiabin da take yini da shi a jikinta.

Tana fatan za a yi amfani da shi a sauran asibitoci, sai dai hukumar inshorar lafiya ta ce hakan zai zama bisa radin kan ma'aikata.

Miss Roslan tana aiki ne a Lincolnshire, ta fara tunanin yin hijabin a lokacin da take daliba mai aiki da asibitin koyarwa na Derby.

'Ina amfani da hijabi ko dankwali guda daya tun safe har lokacin tashi daga aiki, wanda ka iya datti.''

''Ba na jin dadi sosai, sai na yi ta tsarguwa, kuma ba na iya cirewa a lokacin da muke dakin tiyata akwai lokacin da dole na fita don kariya daga daukar cuta,'' in ji Roslan a hirarta da BBC.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ms Tierney ce take horas da Ms Roslana asibitin Royal Derby don sanin makamar aiki

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ta ce dole a samar da wata hanya da za a suturta jiki, ta hanyar koyarwar addinin da mutum yake bi musamman a dakin tiyata da kankanin abu ka iya janyowa mara lafiya wata cuta ta daban.

Miss Roslan dai 'yar kasar Malaysia ce, kuma daga can ta fara kirkirar hijabin da yin gwaji.

''Ina farin ciki da fatan wannan tsari zai samu karbuwa a sauran asibitoci ga wanda yake sha'awar yin hakan.''

Kwararriyar likitar fida Dr Gill Tierney, wadda ke bai wa Roslan horo, ta ce wannan shi ne karon farko da aka kirkiri abu irin hakan na amfani da dankwali ko hijabi a asibitin Birtaniya.

''Ka san yawanci ba a cika magana a kan batutuwan da suka shafi dakin tiyata ba a kasar nan, kuma ba na jin ana kokarin kawo sauyi.''

''Ba wani tsada ne da shi ba, ina kuma fatan za a yi amfani da shi,'' in ji Dr Tierney.

A karon farko a watan a farkon watan Disamba, inshorar lafiya ta asibitin koyarwa na Berby da Burson, sun amince likitoci mata su yi amfani da dankwali ko hijabi a cikin asibiti.