Ana rububin dan Najeriya a Premier, Ozil zai bar Arsenal

Tauraruwar Dennis na haskawa sosai a gasar Zakarun Turai
Bayanan hoto,

Tauraruwar Dennis na haskawa sosai a gasar Zakarun Turai

Club Bruges na Belgium na neman yuro miliyan 30 ga dan wasan gabanta Emmanuel Dennis na Najeriya. (Foot Mercato, via Leicester Mercury)

Dennis a yanzu na daga cikin 'yan wasan gaba da ke haskawa sosai a Turai, ya kuma ja hankalin kungiyoyi musamman a karawar kungiyarsa da Real Madrid inda ya ci kwallaye biyu.

Dan wasan tsakiyar Arsenal Mesut Ozil zai tafi Fenerbahce a matsayin aro na watanni shida a watan Janairu. (Fotomac, via Football.London)

Manchester United ba za ta bari dan wasan tsakiyar Faransa Paul Pogba ya tafi Real Madrid ba a watan Disamba. (Mail).

To sai dai wata majiya na cewa United din na tunanin Pogba ya gama wasa da kungiyar kuma zai kama gabansa a watan Janairu. (Mirror).

Ana sa ran da zarar Carlo Ancelotti ya fara aiki a Everton ba da wata-wata ba zai yi kokarin kulla yarjejeniya da Zlatan Ibrahimovic dan kasar Sweden (Calcio Mercato).

Har yanzu Manchester City da makwabciyarta United ba su cire rai wurin kokarin kulla yarjejniya da Kai Havartz na Jamus ba. (Manchester Evening News).

Rahotanni sun ce dan wasan gaban Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da wasu 'yan wasa sun fara tunanin makomarsu a Arsenal. (Independent).

Tuni kungiyoyin Leicester da Brighton da Southampton suka nuna sha'awar taya matashin dan wasan. (Foot Mercato, via Leicester Mercury).

Akwai yiwuwar tsohon dan wasan tsakiyar Liverpool Emre Can ya bar Juventus saboda rashin samun damar buga wasanni.(Goal).