Ganduje ya ce an bukace shi ya tsige Sarkin Kano

Gwamna Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi II
Bayanan hoto,

Gamayyar kungiyoyin da suka yi kiran sun bukaci Ganduje da ya tsige Sarkin na Kano domin ci gaban jihar

An bukaci Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje da ya gaggauta fara shirin tsige Sarkin Kano Muhammdu Sanusi II, domin kare doka da oda da kuma ikon da masu zabe na jihar suka ba shi.

Babban Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis wadda a ciki ya ce wata gamayya ta kungiyoyin farar hula ne 35, karkashin sunan UMBRELLA OF KANO CONCERNED CIVIL SOCIETY GROUPS, suka bukaci hakan a wata wasika da suka aika wa gwamnan.

A sanarwar sakataren ya bayyana cewa gamayyar kungiyoyin ta ce tana lura tare da nazarin yadda al'amuran jihar suke kasancewa musamman a wannan lokaci, dangane da dambarwar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar da kuma Sarkin Kanon.

Sanarwara ta ce kungiyoyin sun tunatar da shi game da abubuwan da suka bijiro bayan da babbar kotun jihar Kanon ta soke dokar Majalisar Sarakunan Gargajiya jihar, wadda Majalisar Dokokin jihar ta yi,

Hukuncin da a karshe ya bayar da damar yin wata sabuwar dokar, da ta kai ga kirkiro Karin masarautu hudu masu daraja ta daya, dokar da kuma ta ba wa gwamnan damar daukar matakin ladabtar da duk wani sarki da ya saba ta.

Asalin hoton, TANKO YAKASAI

Takardar bayanin da ta fito daga Sakataren Yada Labaran na gwamna ta ce, shugaban gamayyar kungiyoyin Kwamared Ibrahim Ali ne ya sanya hannu a wasikar da aka aika wa gwamnan, inda a ciki kungiyoyin suke nuna takaicinsu da matakin shari'a da aka ce wai masu nada sarki daga daya daga cikin masarautun biyar da dokar ta kafa suka kalubalanta.

Anwar ya ce wasikar ta kuma nuna takaicin yadda wadanda ke kiran kansu dattawan jihar, wadanda suke suka da cewa an yi dokar ne da nufin bata tarihin masarautar Kano na shekara 1000 su suka shigar da karar ta biyu.

Jami'in ya bayyana a sanarwar mai dauke da sa hannunsa cewa bayan da gamayyar kungiyoyin ta bayyana dukkanin fannonin da ake da sabanin, ta ce abin da Sarkin Kanon yake yi na kin martaba gwamnatin jihar Kano da hukumominta,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masarautar Kano ta musanta zarge-zargen facaka da kudin da aka yi wa Sarki Muhammadu Sanusi na II

Ba kawai ya saba wa tsarin mulki ba, wani yunkuri ne na yi wa gwamnatin kishiya, wanda suka ce ba wani shugabanci da ya san abin da yake yi da zai lamunta da hakan, ya bari ya ci gaba.

Ya ce 'yan kungiyoyin sun kuma yi watsi da ikirarin masu kiran kansu dattawan Kanon wadanda ke neman haifar da rudani.

Wasikar gamayyar a cewar sanarwar Babban Sakataren yada labaran na gwamnan na Kano ta yi kira ga gwaman jihar da ya hanzarta tabbatar da ganin Majalisar Masarautun ta fara aiki, sakamakon hukuncin babbar kotun jihar na baya bayan nan.

Takardar kungiyoyin ta kuma ce a cewar sanarwar Sakataren, idan Sarkin Kanon ya ki yin biyayya ga gwamnatin Kano, to sun bukaci gwamnan da ya hanzarta yin amfani da tanadin dokar Masarautun ta 2019, domin ciyar da jihar gaba.