'Yan majalisar Amurka sun dinke baraka

Nancy Pelosi

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

Shugabar majalisar wakilan Amurka, Ms Nancy Pelosi 'yar jam'iyyar Democrat

Wannnan Yarjejeniyar ta maye gurbin yarjejeniyar kasuwanci maras shinge ta nahiyar Amurka ta Arewa, ta 1994, wadda Shugaba Trump ya yi alkawarin sake tattaunawa a kanta a lokacin yakin neman zaben 2016.

Duk da kasancewar dokar ko yarjejeniyar mai muhimmancin siyasa ga Donald Trump, ta kasance a majalisar wakilan tsawon wata da watanni.

Yanzu kuma sai ga shi kwana daya bayan tsige shugaban da majalisar wakilan ta yi, ta amince da dokar, da goyon bayan jamiyyun biyu, wadanda suka rabu kowa ya ja bangarensa, a kan batun tsige shugaban.

Dukkanin bangarorin biyu, 'yan Democrats da 'yan Republicans sun manta da bambance-bambancen da ke tsakaninsu suka amince cewa mataki ne da zai amfani tattalin arzikin Amurka.

Yarjejeniya ce da ta shafi harkokin kasuwanci na fannin fasaha, ta sanya ka'idoji masu tsanani na kwadago da kare muhalli, sannan kuma ta bude kasuwar kayayyakin da suka jibanci madara ga manoman Amurka.

A farkon shekara mai kamawa ne 'yan majalisar dattawan Amurkar za su kada kuri'arsu su kuma a kan yarjejeniyar.

Shugabar majalisa wakilan, Nancy Pelosi, ta ce amfanin da yarjeniyar za ta yi wa ma'aikatan Amurka ya fi muhimmanci, ga duk wani goyon baya da 'yan Democrat za su bayar na dokar, da zai ba wa Mista Trump.

A wani sakon twitter Mista Trump ya ce Ms Pelosi ba ta da wata masaniya a kana bin da yarjejeniyar ta kunsa, kawai tana son ta samu yabon da bai kamace ta ba a kan amincewa da yarjejeniyar.

Shugaban Mexico Lopez Obrador ya ce amincewa da yarjejeniyar labara ne mai dadin ji.