'Wasu mazan ba sa haihuwa ko da kuwa an ga matansu da ciki’

Bayanan sauti

Shirin Lafiya Zinariya

Ku latsa wannan alamar lasifikar domin sauraron shirin Lafiya Zinariya da Habiba Adamu:

Wani bincike da hukumar ta gudanar kan yawan al'umma a shekarar 2004 ya nuna cewa, kimanin kashi 30 cikin dari na mata masu shekara 25 zuwa 49 ne, ke fama da matsalar rashin haihuwa bayan sun taba samun haihuwa sau daya, a kasashen da ke kudu da Sahara a nahiyar Afrika.

Ko da yake hukumar ta ce duk da cewa a tsakanin ma'aurata kashi 50 cikin dari da matsalar rashin haihuwa ta shafa, an gano cewa matsalar daga wajen maza ta ke.

To sai dai a al'adance an fi dora laifin ne a kan mata.

Lamarin da kan janyo wa mata kyara da tsangwama da wariya daga abokan zama, dangi da kuma al'ummar da suke zaune a ciki.

Sai dai a Najeriya daya daga cikin kasashen da wasu daga cikin mutanenta ke fuskantar wannan matsala, hukumomin 'yan sanda sun sha kai samame tare da cafke gwamman matan da aka ajiye a wasu wurare domin yi musu ciki daga bisani a sayar da jariransu.

'Yan sanda sun yi zargin cewa cikin masu sayen jariran har da wasu wadanda ke fuskantar matsalar rashin haihuwa, inda wasu ma a cewar hukumomi su kan zo sayen irin wadannan jarirai ne daga makwabtan kasashe.

A bayyane take cewa wasu matan kan shiga wani hali saboda rashin haihuwa, lamarin da kan sa su bi wasu hanyoyin da ba su dace ba domin magance matsalar.

Sashen Hausa na BBC ya duba yadda wannan matsala ta rashin haihuwa ta ke a likitance, domin fadakar da al'umma tare da nuna musu cewa akwai hanyoyi da masu wannan matsala za su iya bi a likitance don samun dacewa.