APC na neman mafita kan rikicin cikin gida

  • Ibrahim Isa
  • BBC Hausa
Shugabannin jam'iyyar APC

Asalin hoton, @OfficialAPCNg

Bayanan hoto,

Daga dama zuwa hagu: Oshiomole (a tsaye), Shugaba Buhari, Farfesa Osinbajo, Bola Tinubu a wurin taron manema labarai bayan dage zaben 2019

Jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban Majalisar Dattawan kasar domin sulhunta tsakanin `ya`yanta sakamakon wasu korafe-korafen da suke yi.

A `yan kwanakin nan, wasu shugabannin jam`iyyar na jihohi sun bukaci shugaban jam`iyyar na kasa, Adams Oshiomole da ya yi murabus.

Wasu dai na ganin rikicin yana da alaka da kokuwar da aka fara ta neman shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam`iyyar a zaben shekara ta 2023.

Jam`iyyar APC ta bayyana cewa ta kafa kwamitin ne karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawan, Ahmed Lawan, domin gano masu kukan gaskiya da na gangan saboda daidaita tafiyar jam`iyyar.

Alhaji Ibrahim Masari shi ne babban jami`in walwalar jam`iyyar na kasa kuma ya shaida wa BBC cewa cikar da jam'iyyar tasu ta yi kuma ta batse ne dalilin yin irin wannnan korafi.

"Ka san duk inda jam'iyya ta cika ta batse za ka samu irin wadannan korafe-korafe. A wurin taron da muka yi ne aka kafa kwamitin domin jin korafe-korafen," Ibrahim Masari ya fada.

"Ita wuta tun tanba karama ake sa ruwa rabin kofi a kashe ta. ba zan ce korafe-korafen ba su da inganci ba amma dai ba za su fi karfin kwamitin ba."

Duk da cewa jam`iyyar APC ba ta fito ta fayyace irin rigingimun da take fama da su ba, abubuwan da suka bayyana a zahiri na nuna cewa tana fama da matsaloli ne da suka shafi shugabanci.

Tun bayan babban zaben kasar da aka yi a farkon wannan shekarar, wasu suka fara sukar shugaban jam`iyyar na kasa, Adams Oshiomole suna cewa ya kamata ya sauka daga mukaminsa.

Hakan ya biyo bayan nasarar kwace wasu kujerun gwamna da jam'iyyar hamayya ta PDP ta samu a kan APC.

Wata ruwayar kuma ta nuna cewa akwai rashin jituwa a tsakanin shugaban jam`iyyar na kasa da wasu gwamnoni `ya`yan jam`iyyar, kasancewar ba ya daga masu kafa su taka rawarsu da jagororin jam`iyyar a matakin jiha.

Lamarin ya kara takun-sakar da ke tsakaninsa da shugabannin jam`iyyar na jihohi.

Asalin hoton, @OfficialAPCNg

Bayanan hoto,

Wasu na ganin takarar 2023 ce ta fara zafafa tun yanzu

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu kuma na danganta sabon rikicin da batun wanda zai kasance dan takarar jam`iyyar a babban zaben Najeriya na shekara ta 2023.

Har wa yau, wasu na cewa an samu rarrabuwar kawuna a tsakanin manyan jigogin jam`iyyar, kasancewar inda shugaba Oshiomole da wasu suka karkata daban, yayin da wasu gwamnoni da ministoci suke da nasu gwamnan daban.

Wannan ne ma ya sa wasu masana siyasa irin su Farfesa Jibrin Ibrahim na cibiyar bunkasa demokuradiyya ta CDD ke ganin cewa za a iya warware rikicin APC, amma sai shugabanta na kasa ya dinga cizawa yana hurawa.

"Abin da shugaban jam'iyyar yake aikatawa yana jawo rikici daban-daban. Duk abin da ya yanke babu mai ja da shi. Wadanda suka ja da shi kuma sai a yi kokarin cire su daga mukamansu.

"Idan bai canza wannan hali nasa ba ban ga yadda za a gyara abubuwan ba," In ji Jibrin Ibrahim.

Jam`iyyar APC ta fuskanci irin wannan matsalar gabanin babban zaben da ya wuce har ta kafa irin wannan kwamitin sasantawar karkashin jagorancin Bola Ahmed Tunubu, wanda wasu ke cewa aikin da kwamitin ya yi ba yabo ba fallasa.

Don haka ne wasu ke kaulani game da tsairin da wannan sabon kwamitin, karkashin jagorancin senata Ahmed Lawan zai yi. Amma Alhaji Ibrahim Masari ya ce ba ya shakkar lamarinsa.

Rikicin shugabancin jam`iyya mai mulki dai ba sabon abu ba ne a Najeriya.

Hatta babbar jam`iyyar hamayyar kasar, wato PDP ta yi irin wannan faman a baya, har ta kai ga sai da aka sauya shugabannin jam`iyyar na kasa har sau uku a cikin shekara daya.