Masarautar Kano: Ba mu ce a tsige Sarki Sanusi ba – KCSF

Sarki Sanusi da Ganduje

Asalin hoton, Kano Government

Gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Kano ta nisanta kan ta daga wata wasika da ke cewa kungiyar ta yi kira ga gwamnan Kano ya tsige Sarki Muhammadsu Sanusi II daga kujerarsa.

Tun farko dai sakataren yada labaran gwamnatin jihar ne Abba Anwar ya fitar da sanarwa cewa kungiyar ta rubuta masu wasika tana neman Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya yi hakan.

A wata sanarwa da ta fitar a yau Juma'a, Kano Civil Society Forum (KCSF) ta ce "kage aka yi mana domin bata mata mana suna".

Ta kara da cewa: "Abin takaici ne yadda wasu mutane da ba su bayyana kan su ba suka yi amfani da sunan kungiyar suka nemi gwamnan ya cire sarki daga mukaminsa.

"Bisa wannan dalili ne muke amfani da wannan damar domin nisanta kammu daga wannan batu na wasu kungiyoyi marasa kan-gado."

Wannan na zuwa ne rana guda da wata sanarwar ta fito daga masarautar Kano, wadda ke cewa Sarki Sanusi ya karbi mukamin Shugabancin Majalisar Sarakunan Kano da Ganduje ya nada shi.