'Yan majalisa sun amince Birtaniya ta fice daga EU da gagarumin rinjaye

Boris Johnson

Majalisar dokokin Birtaniya ta jefa kuri'ar amincewa da dokar ficewar kasar daga Tarayyar Turai bayan kusan shekaru 50, da gagarumin rinjaye.

Kwanaki takwas bayan lashe zaben Jam'iyyar Conservative ta Boris Johnson ya kawo karshen tayar da jijiyoyin wuya ake yi kan batun a majalisar tun bayan kuri'a raba gardamar da aka yi a 2016.

'Yan majalisar shida daga jam'iyyar adawa ta Labour sun goyi bayan gwamnati a kuri'a, suna cewa sun amsa kiran da mazabunsu suka yi musu na su amince da ficewar kowa ya huta.

Yanzu dai za a tura dokar zuwa majalisar dattawa domin su yi muhawara a kai kafin gwamnati ta shiga tattaunawa da EU din don daddale magana kan ficewar.