ICC ta bukaci a binciki laifukan yaki da ake zargin Isra'ila a Gaza

Kotun ICC ta dade tana duba karar da Palastinawa suka shigar tun shekarar 2015

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kotun ICC ta dade tana duba karar da Falastinawa suka shigar tun shekarar 2015

Babbar mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC ta ce tana son a gudanar da bincike a bayyane kan zargin aikata laifukan yaki a wasu yankunan Falasdinawa.

Fatou Bensouda ta ce an aikata laifuffukan yakin a Yamma gabar Kogin Jordan da gasbashin birnin kudus da kuma zirin Gaza inda kuma ta bukaci kotun ta yanke hukunci bisa ikon kotun.

Kotun ICC dai ta dade tana duba karar da Falastinawa suka shigar tun shekarar 2015.

Sai dai Isra'ila ta kira yunkurin kotun ICC din a matsayin wanda ba shi da tushe bare makama.

Cikin wata sanarwa, Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce ICC ba ta da hurumin sauraron karar kuma matakin ya siyasantar da kotun ta Hague wajen soke ikon kasar Isra'ila.

Isra'ila dai ta mamaye yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da Gaza da kuma gabashin birnin Kudus a yakin da aka gwabza a gabas ta tsakiya a shekarar 1967.

A hukuncin da ta yanke, Bensouda ta ce binciken farko-farko da aka gudanar ya tattara bayanan da ake bukata na fara binciken a bayyane tana mai cewa ta "gamsu cewa akwai hujja da za ta bada damar gudanar da binciken."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cewarta, babu wasu dalilai na cewa binciken ba zai yi wa al'ummar Falastinu adalci ba sannan ta kara da cewa ta gabatar da bukatar alkalai su yanke hukunci kan yankin da binciken da za a gudanar zai shafa saboda batutuwa na shari'a game da yankunan.

Sai dai kuma babu tabbaci kan ko yaushe za a dauki mataki amma Bensouda ta ce ta nemi alkalan kotun su yanke hukunci domin bai wa ofishinta damar daukan matakin da ya dace.

Babbar mai gabatar da karar a kotun ICCn ba ta fadi ko su wane ne wadanda suka aikata laifukan yakin ba, sai dai idan ta gabatar da binciken, akwai tuhume-tuhumen da za a iya yi wa Isra'ila da Falsatinawa kamar yadda wasu rahotanni suka shaida.

Ita dai Bensouda ta mayar da hankali ne kan binciken farko-farko da aka gudanar kan karar da Falastinawa suka shigar game da yadda Isra'ila ta yi gine-gine a yankunanta da kuma kasancewar sojojinta a Gaza.

Kotun ICC din tana duba abin da Falastinawan suka kira laifukan yaki da Isra'ila ta aikata tun Yunin 2014, wata guda kafin wani yaki tsakanin Isra'ila da 'yan tawayen Falasdinawa a Gaza.

A yakin, an kashe Palastinawa 2,251 har da fararen hula 1,462 yayin da sojoji 67 da kuma farar hula 6 suka mutu a bangaren Isra'ila.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Fatou Bensouda, babbar mai gabatar da kara a kotun ICC

Mista Netanyahu ya bayyana sanarwar a matsayin matakin ba-zata inda ya bayyana cewa ICC tana da hurumi ne kawai kan korafe-korafen da kasashe suka gabatar mata amma a cewar shi, babu wata kasa Falasdinu.

Tun da farko, Atoni Janar na Isra'ilar ya ce ICC ba ta da hurumi da gabar kogin Jordan ko Gaza.

Isra'ilan kuma tana kallon gabashin Kudus a matsayin yankinta wanda shi ma ta ce ba ya karkashin hurumin kotun.

Falasdinawa dai na neman kafa gabashin Kudus ya kasance a matsayin babban birnin kasar.

Cikin wata sanarwa, gwamnatin Falasdinawa ta ce "tana maraba da wannan matakin na gudanar da bincike bayan shafe kusan shekara biyar ana duba batun."

Sai dai wata kungiyar kare hakkin bil adama a Isra'ila, B'Tselem ta ce "zame-zamen da Isra'ila ta ke yi ba zai hana kokarin da kasashen duniya suke ba na ganin an dauki matakin shari'a da zai hukunta ta".

Akwai gine-ginen Isra'ila 140 a gabar kogin Jordan da gabashin birnin Kudus wanda kasashen duniya suka kira haramtattu - abin da Isra'ilan ta musanta kuma a watan da ya gabata ma Amurka ta sanar da matakinta inda ta ce ba ta yi wa gine-ginen kallon wadanda aka gina ba bisa ka'ida ba.