Darikar Kadiriyya ta haura 'shekara 900 da kafuwa'

Latsa alamar lasifika domin sauraren hirar

A yayin wata hira da BBC, shugaban kungiyar Kadariyya na Afrika Sheikh Karibullah Sheikh Nasir Kabara, ya ce kungiyar ta samo asali ne tun zamanin Sheikh Abdulkadir Jilani wanda ya assasa ta shekaru da dama.

Ya ce ana gudanar da bikin Maukibi domin tunawa da Sheikh Abdulkadir Jailani da kuma tunatar da jama'a kan hidimarsa ga addinin Islama.

Ya kuma ce Sufaye na dariku ne suka yi sanadin shigowar musulunci a yankin nahiyar Afrika. Kuma a cewarsa "Sheikh Usman Danfodio, ya yi jihadinsa da tutar Kadiriyya."

Kungiyar dai na daya daga cikin kungiyoyin addinin musulunci da suka fi tasiri a kasashen yammacin Afrika, ko da yake tana da dumbin mabiya a sauran kasashen duniya daban-daban.