An kashe fursunoni 18 a rikicin gidan yarin Honduras

Dakarun gwamnatin da aka tura a wannan makon domin yin aiki a gidajen yari a Honduras

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dakarun gwamnatin da aka tura a wannan makon domin yin aiki a gidajen yari a Honduras

Akalla fursuna 18 ne aka kashe a wani tashin-tashinan da ya kaure tsakanin bangarorin gaggan fursunoni a wani kurkuku a Honduras.

Ricikin shi ne mafi munin rigingimun da aka samu a gidajen yarin kasar a baya bayan nan.

Fada ya kaure ne bayan wani rikice-rikicen da aka samu a fadin kasar mai fama da cinkoso fiye da misali a gidajen yari.

Kakakin rundunar tsaron kasar ta Fusina Antonio Coello, ya tabbtar wa 'yan jarida mutuwar mutuwar fursunonin.

Kimanin mutum 20,000 ne ke tsare a gidajen yari nakasar da aka gina domin su dauki mutum 8,000.

Rikicin na zuwa ne bayan a ranar Laraba gwamnatin Honduras ta kafa dokar ta baci kan gidajen yarinta da kuma mayar da gudanar da su a hannun dakarun soji.

Wani jami'in sojin kasar ya ce rikicin ya fara ne gabanin sojoji su karbi gudanar da gidan yarin da ke birnin na Tela mai makwabtaka da teku ba.

Tuni dai ake girke jami'an tsaro domin kwantar da tashin hankalin, a cewar hukumomin Honduras.

Akan samu rigingimu neman nuna karfin iko a tsakanin gungun fursunoni a gidajen yarin kasar.