Syria: An kashe fararen hula 12 a Idlib

Hakkin mallakar hotoAFP

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mutum 8 daga cikin mamatan an kashesu ne a birnin Saraqib

Fararen hula akalla 12 sun mutu a wani harin sama a yankin Idlib da ke karkashin ikon masu tada kayar baya a Syria.

Mutum 8 daga cikin mamatan an kashesu ne a birnin Saraqib.

Ana cigaba da fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tayar da kayar baya a yankin kudu maso gabashin Syria, a cewar kungiyar kare hakkin an adam ta Syrian Observatory for Human rights da ke da mazauni a Birntaniya.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane daga bangarorin biyu, da ke cigaba da yakar juna cikin 'yan kwanakin da suka wuce.

Hakan ya kuma tilasta wa dubunnan mutane tserewa daga gidajensu

Dakarun gwamnatin Syria na samun goyon bayan Rasha a yunkurinsu na sake kame yankin na Idlib daga hannun babbar kungiyar masu tada kayar baya a yankin, wadda ke da alaka da kungiyar al-Qaeda.