Iskar Gas: Jamus ta juya wa Amurka baya saboda Rasha

Butun iskar gas na Nord Stream Two na Rasha

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Butun iskar gas na Nord Stream Two na Rasha

Jamus ta bi sahun Rasha wajen yin tir da matakin da Amurka da dauka na sanya wa takunkumi a kan shirin Rasha na shimfida bututun iskar gas daga Rasha zuwa Jamus.

Mai magana da yawun Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel ta yi watsi da takunkumin da cewa za su yiwa kamfanonin Jamus da ma na Tarayyar Turai illa matuka.

Angela Markel ta bayyana takunkumin na Amurka a kan shirin da aka fi sani da suna Nord Stream Two gas pipeline, a matsayin katsalandan ga harkokin cikin gidan Jamus.

Tuni dai Rasha da makwabciyarta Ukraine suka rattaba hannu kan yarjejeniyar amfani da bututun gas din.

Bututun wanda Rasha za ta yi amani da shi wurin aikawa da iskar gas zuwa Tarayyar Turai na tsawon shekara biyar ya ratsa ne ta cikin Ukraine domin.

Yarjejeniyar ta kunshi tsabar kudi dala biliyan 2.9 da Rashan ta biya Ukraine domin biyan wasu batutuwan sarkakiyar sharia tsakanin kasashen biyu.

Rasha Ukraine sun kuma amince da tsarin damar sake tsawaita yarjejeniyar 5 da karin shekara goma.

Masu sharshi na kallon hakan a matsayin babban cigaban dangantaka tsakanin makwabtan biyu masu gaba da juna.

Takun saka tsakanin kasashen ya biyo bayan matakin Rasha na mamaye yankin Crimea da ke Ukraine zuwa karkashin ikonta a cikin shekara ta 2014.

Kazalika matakin Rasha na nuna goyn bayanta ga 'yan aware a gabashin Ukraine.