An yanke wa wanda ya zagi Manzon Allah hukuncin kisa

@

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An tsaurara matakan tsaro a gidan yarin da ake tsare da Junaid Hafeez, wanda ke kusa da kotun da aka yanke masa hukunci

An yanke wa wani malamin jami'an da ya yi batanci ga Annabi Muhammad SAW a shafinsa na sada zumunta hukuncin kisa.

Malamain jami'ar mai suna Junaid Hafeez, yana tsare ne a hannun hukuma bayan ya wallafa kalaman cin mutunci ga Manzon Allah a kafafen sada zumunta a 2013.

Hukumomin Pakistan ba sa wasa da duk abin da ya shafi batanci ga addini.

Zargin yin batanci ga addini kan jefa wadanda ake tuhuma cikin hadari a kasar.

A 2014 ne aka harbe lauyan da ke kare Junaid wato Rashid Rehman, bayan ya amince ya kare wanda ake zargin.

Junaid ya shafe shekaru a killace shi kadai a gidan yarin da ake tsare da shi bayan karuwar farmakin da wasu fursunoni ke kai masa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Lauyoyin masu shigar da kara na rabon alawa saboda murna bayan kotu ta yanke hukunci

Lauyan da ke kare Junaid a yanzu Asad Jamal ya ce hukuncin da kotun ta yanke abin takaici ne kuma za su daukaka kara.

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty ta yi zargin rashin adalci a hukuncin, wanda ta bayyana a matsayin "mai ban mamaki da ban takaici".

Me dokar Pakistan ta ce game da batanci ga addini?

Pakistan na da tsauraran dokoki kan masu batanci ga addini. Doka ta tanadi hukuncin kisa ga masu batanci ga addinin Islama.

Turawan mulkin mallaka na Birtaniya ne suka fara yin dokokin a 1869, sannan a kara fadada su a 1927.

Bayan samun 'yancin kai daga Indiya a 1947, sai Pakistan ta ci gaba da amfani da dokokin.

Dokokin sun haramta kawo tarnaki ga tarukan addini da wucewa ta makabartu ba bisa ka'ida ba da yin batanci ga addini ko akidu da kuma yin gangancin keta hurumin wuraren ibada ko ababen bauta.

Da farko dokar ta yi tanadin daurin shekara daya zuwa 10 ga masu laifin.

Amma gwamnatin sojin kasar ta 1980 zuwa 1986, karkashin Janar Zia-ul Haq, ta sauya wasu tanade-tanaden dokar.

A yunkurinsa na mayar da Pakistan kasar Musulunci a 1973, Janar Haq ya ayyana mabiya akidar Ahmadiya a matsayin wadanda ba Musulmai ba sannan ya tsame su daga al'ummar Musulmin kasar mafiya rinjaye.

Sabuwar dokar da ya yi ta haramta cin mutuncin malaman addini sannan ya sanya hukuncin kisa ga masu wulakanta Kur'ani.

Daga bisani ya sanya hukuncin kisa ko daurin rai da rai ga duk wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad.

Zuwa yanzu mutum 40 ne ke tsare a kasar bayan yanke masu hukuncin daurin rai da rai saboda batanci - amma babu wanda aka zartar wa da hukuncin kisa.

Kasashen duniya sun fara sa ido ne kan dokar batanci a Pakistan bayan da a shekarar 2018 kotun kolin kasar ta soke hukuncin daurin da aka yi wa wata mata Kirista da ta shafe shekara takwas a gidan yari saboda zarginta da zagin Manzon Allah.

Sakin matar mai suna Asia Bibi ya haifar da zanga-zanga a fadin Pakistan abin da ya sa Bibi barin kasar.