Yadda aka kama wasu 'yan Najeriya a Bosnia

Uchenna Abia da Kenneth Eboh a hoton da suka dauka da mambobin hukumar kula da 'yan Najeria mazauna kasashen waje

Asalin hoton, Nigerians in Diaspora Commission

Bayanan hoto,

Kenneth Eboh da Uchenna Abia (na uku da na biyu daga hannun hagu) a wani hoto da hukumar kula da 'yan Najeria mazauna kasashen waje ta fitar

Wasu 'yan wasan kwallon Tennis 'yan asalin Najeriya da suka ce an mika su Bosnia-Herzegovina bayan da 'yan sandan Croatia suka dauka bakin haure ne, sun dawo Najeriya.

Uchenna Abia da Kenneth Eboh sun shaida wa BBC irin farin cikin da suke ciki bayan sun dawo a gida.

Daliban sun je Croatia ne domin buga kwallon Tennis a watan da ya gabata sai dai 'yan sandan kasar sun kwashe su zuwa Bosnia inda aka tsare su a wani sansanin da ake ajiye bakin haure.

Ma'aikatar cikin gida ta Croatia ta ce ba ta da masaniya kan yadda mutanen biyu suka tsinci kansu a Bosnia.

Abin da ya faru

Mista Abia da Mista Eboh dai sun shiga Croatia ne bisa ka'ida cikin watan da ya gabata domin shiga gasar dalibai ta kwallon Tennis a birnin Pula.

Sun ce suna tsaka da yin tattaki a babban birnin Zagreb gabanin komawarsu Najeriya kamar yadda aka tsara, sai 'yan sandan Croatia suka kama su suka kuma suka yi awon gaba da su zuwa kan iyakar kasar tare da tilasta musu shiga Bosnia.

Mista Eboh ya fada wa BBC cewa 'yan sandan sun "tilasta musu shiga wani daji a Bosnia."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cewarsa "ba mu da wani zabi saboda sun yi yunkurin harbinmu."

"Sun ce mu 'yan Bosnia ne don haka dole ku je Bosnia'' In ji Mista Eboh.

Daliban sun ce kokarin da suka yi na yi wa jami'an bayani cewa suna da takardar bizarsu ya ci tura.

Mista Eboh ya kara da cewa ba su san dalilin da ya sa suka tafi da su wata kasar ba da tsakar dare.

An dai tsare daliban ne a wani sansani da ke kusa da birnin Velika Kladas da ke iyaka da kasar Croatia inda suka ce a wajen aka kwace musu wayoyinsu.

Bosnia dai babbar hanya ce ta shiga Tarayyar Turai inda 'yan ci-rani 45,000 suka isa kasar tun farkon shekarar 2018.

Kungiyoyin bada agaji sun yi gargadin samun annoba a kasar inda ake fama da sanyi ba tare da mutane suna da muhalli ba.

Shi kuwa Mista Abia ya bayyana mutanen Bosnia a matsayin masu haba-haba da mutane yana mai cewa sun godewa masu aikin sa-kai na kasar da suka ziyarce su tare da ba su abinci.

Bayan komawarsa Najeriya ranar Asabar, Mista Abia ya ce yanzu yana jinsa a sake kuma cikin tsaro.

Gwamnatin Croatia dai ta musanta zarge-zargen tana mai cewa daliban sun yi batan dabo ne bayan da suka fita daga otel din da suka sauka.

Kakakin wata ma'aikata a kasar ya ce jami'ai na sake duba batun don gano ko sun yi yunkuri ne wajen yin amfani da gasar da suka je domin samar wa kansu wajen zama a Turai, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar, Hina.

Dubban bakin haure da suka yi kokarin shiga Tarayyar Turai ta kasar Croatia sun yi zargin cewa 'yan sandan Croatia sun ci zarafinsu tare da kora su Bosnia da karfi.