Amurka ta saka Najeriya cikin kasashen da ke take hakkin addini

Jami'an tsaron Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnan Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da za ta sanya wa ido bisa zargin take hakkin kowane mutum na yin addinin da ya ga dama ba tare da wata tsangwama ba.

Wannan ne dai karon farko da sunan Najeriya ya fito a rukunin kasashen da hukumar kare 'yancin yin addini ta Amurka ta saba fitarwa a kowace shekara.

Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ne ya sanar da sanya Najeriya a jerin kasashen.

Mista Pompeo ya fitar da sanarwar ne bayan fitar da rahoton hukumar kare 'yancin yin addini ta Amurka kan kasashen da gwamnatin kasar ke sanya wa ido kan take hakki addinin.

Rahoton na 2019 ya fadi dalilan saka sunan Najeriya a jerin kasashen da suka kunshi har da Iran da Koriya ta Arewa da Paskistan da kuma Rasha.

Sai dai zuwa yanzu babu wani martani da ya fito daga fadar gwamnatin Najeriya game da matakin na Amurka.

A bana ne aka kara sunayen Najeriya da Sudan da Cuba da Nicaragua a jerin kasashen.

Kasashe irinsu Burma da China da Eritrea da Iran da Koriya ta Arewa da Pakistan da Saudiyya da Tajikistan da kuma Turkmenistan an sake sanya sunayensu ne a jerin kasashen da ke take hakkin gudanar da addini.

An kuma sabunta matsayin kasashe da Amurka ke sanya wa ido kamar Rasha da Uzbekistan da Comoros.

Amurka kuma ta ce ta bayyana kungiyoyi masu da'awar jihadi kamar al-Nusra Front da al-Qa'ida da al-Shabab da Boko Haram da 'yan Houthi da ISIS da kuma Taliban a matsayin babbar damuwa ga keta hakkin gudanar da addini.

Dalilin saka Najeriya

Wannan ne dai karon farko da Najeriya ta fito cikin rukunin kasashen da Amuka ta ce za ta sanya wa ido domin tabbatar da kare yancin kowanne mutum da ke son bin dukkanin addinin da ya ga dama a kasar.

Rahoton da hukumar kiyaye yancin yin addini ta Amurka ta fitar ya ce a shekarar 2018 'yancin yin addini a Najeriya ya samu gagarumin tasgaro, saboda yadda gwamnati ta nade kafa , duk da tsangwama da kai hari ga musulmai da kiristoci da ake yi ba tare da ta dauki mataki, ko ma hukunta wadanda ke da alhakin yin hakan ba.

Kazalika kungiyar Boko Haram da takwarar ta ISWAP na ci gaba da hallaka farar hula saboda banbancin ra'ayi ta fuskar addini, duk da ikirarin da hukumomin kasar ke yi na cewa sun ci karfin kungiyoyin da ke da'awar jihadi.

Rahoton ya ambato rikicin kungiyar Ibrahim Elzakzaky, inda Amurka ta ce rundunar sojin Najeriya da hukumomin tsaron kasar na ci gaba da keta hakkinsu na 'yancin gudanar da harkokin su na addini.

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Rahoton ya ce har yanzu ana ci gaba da tsare jagoran kungiyar da mai dakinsa da daruruwan mabiyan sa, da kuma matakin da gwamnatin kasar ta dauka na haramta kungiyar baki daya.

Karin wasu dalilai da Amurka ta ce sun sa ta daukar wannan mataki na bayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da za ta sanya wa ido ta fuskar yancin addinin shi ne, yadda wasu jihohi goma sha biyu na Najeriyar ke gudanar da tsarin shari'ar islama.

Ta ce jihohin sun samar da dokoki da kafa hukumar Hisbah domin tabbatar da aniyar aiwatar da shari'ar musulunci.

Auren wuri ga yara mata, na daga cikin abubuwan da rahoton ya ambata, da ya ce wasu dokoki a irin wadannan jihohi sun yi tanadin wasu shekaru da kowacce 'ya mace za ta iya zaman aure, abin da rahoton ke ganin cewa kan taimaka wajen haifar da matsaloli daga baya.

Amurka ta ce da farko zata bi Najeriya da sauran kasashen da sunan su ya fito a wannan rukuni ta lalalama, amma idan suka gaza magance wannan matsala to kuwa ba ta da wani zabi da ya wuce ta kakaba musu takunkumi kariyar tattalin arziki.