Bayan shakara 43 an yi sabon firai minista a Cuba

An nada Manuel Marrero Cruz (hannun dama) a lokacin zaman majalisar dokokin kasar wanda tsohon shugaba Raúl Castro (hannun hagu) ya halarta

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An nada Manuel Marrero Cruz (hannun dama) a lokacin zaman majalisar dokokin kasar wanda tsohon shugaba Raúl Castro (hannun hagu) ya halarta

An nada sabon firai minista na farko shekara arba'in da uku bayan soke mukamin a lokacin mulkin jagoran juyin juya hali Fidel Castro, a Cuba.

Sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka kaddamar a wannan shekara ne ya dawo da mukamin da Fidel Castro ya soke a shekarar 1976.

Shugaba Miguel Díaz-Canel ya sanar da ministar yawon bude idon kasar Manuel Marrero Cruz a matsayin sabon firai minista.

Mista Marrero mai shekara 56 ne zai cigaba da gudanar da wasu daga cikin harkokin gwamnati da a baya suke karkashin ofishin shugaban kasa.

"Firai minista shi ne zai zama na hannun daman shugaban kasa a gudanar da harkokin gwamnati", a cewar jaridar intanet gwamantin kasar Cubadebate.

Amma masu adawa na ganin bata sauya zane ba, domin har yanzu jam'iyar Cuban Communist Party da sojojin kasar ne ke da wuka da nama a kasar.

Yadda aka nada Sabon firai ministan

Majalisar ministocin kasar ce ta tabbatar da nadin Marrero a matsayin firai minista a ranar Asabar.

Mista Marrero fitaccen dan siyasa ne daga fannin yawon bude ido kuma babban abin dogaron Cuba wurin samun kudaden shiga, acewar jaridar Granma.

A shekarar 2000 Marrero ya jagoranci kamfanin yawon bude ido na Gaviota wanda sojoji ke gudanarwa. Gwamnatin Donald Trump ta Amurka ta sanya wa otal otal din Gaviota takunkumi.

A shekarar 2004 gwamnatin Fidel Castro ta nada Marrero ministan yawon bude ido, inda ya kawo cigaba da bunkasar harkokin yawon bude ido a kasar.

Yanzu babu tabbacin ko firai ministan zai cigaba da gudanar da ma'aikatar.

Yayin nada Marrero a matsasin firai minista shugaba Díaz-Canel ya yaba wa rawar da ya taka wurin kyautata alakar kasar da kamfanonin kasashen waje.

Ya kuma yaba masa a matsayin "mai rikon amana da jajircewa tare da biyayya ga tsarin kwamunisanci da juyin juya halin kasar".

Fidel Castro da Kwamunisanci a Cuba

Fidel Castro ya jagoranci juyin juya halin kwamunisanci a Cuba. Ya hambarar da gwamnatin kasar a 1959 sannan ya ayyana kansa a matsayin firai minista.

Fidel Castro ya rike mukamin har zuwa 1976, sadda aka soke matsayin. Daga nan ya koma shugaban jam'iyyar Communist Party kuma shugaban majalisar zartaswa da ta ministoci.

Bayan rashin lafiyarsa ta tsananta, sai Fidel ya mika mulki ga dan uwansa Raúl a 2006. Fidel ya rasu a shekarar 2016.

Raúl Castro ya yi murabus daga kujerar shugaban kasar a 2018. Amma ya cigaba da zama shugaban jam'iyya kuma kusa a siyasar kasar.