Masarautun Kano: Dattawan Arewa sun fara taron sulhu

Ganduje da Sarki Sanusi

Asalin hoton, SANI MAIKATANGA PHOTOGRAPHY

Bayanan hoto,

Kungiyar ta ce ta samu amincewar dukkanin bangarorin

Kungiyar dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF) ta fara wani taro domin yin sulhu tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Wannan yunkuri nasu na zuwa ne bayan da Sarkin na Kano ya amince da nadin da gwamnan Kano ya yi masa na Shugaban Majalisar Sarakunan jihar.

Sarki Sanusi ya bayyana amincewar ne bayan an aike masa da wasikar neman ko dai ya amince ko kuma akasin haka biyo bayan shurun da ya yi tun da farko.

Dr. Hakim Baba Ahmed na kungiyar NEF ya shaida wa BBC cewa kasancewarsu dattawa, bai kamata a ce sun yi shuru game da lamarin ba yayin da yake kara kara kamari.

"Mun tara dattawan Arewa daga ko'ina domin mu zo mu kawo karshen hayaniya da muka ji ana yi," Hakim Baba ya fada.

Ya ci gaba da cewa: "Mun dade muna magana kawai ji ne dai ba a yi. Sai da muka tabbatar mun samu izinin duk wadanda abin ya shafa sannan muka zo.

"Abin da muka tarar ba shi muke ji a kafafen yada labarai ba. Da muka saurari kalamansu (gwamnati da masararuta) sai muka fahimci cewa ba wani abu ne da za a samu matsala a kai ba.

"Ba ma son abin da zai taba kano domin kuwa muna da matsaloli a Arewa da yawa, wannan abu zai iya kara wa matsalolin yawa.

"Alhamdulillahi ba a boye mana komai ba. Duk abin da muka ji ya yi mana amfani kuma muna so duk abin da za a yi ya zama bisa da'a da al'adummu na Arewa."

Rikici tsakanin gwamnatin Kano da masarauta ya sha daukar salo iri-iri tun bayan da gwamna Ganduje ya kirkiro sababbin masarautu hudu - kari a kan ta Kano.

Rahotanni sun ruwaito cewa an yi kallon-kallo tsakanin sarakunan jihar ranar Alhamis a wurin taron yaye hafsohin 'yan sanda da aka yi a garin Wudil na jihar.