Cikin Hotuna: Ziyarar Emmanuel Macron a Nijar

Ranar Lahadi ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyara kasar Nijar domin yin ta'ziyyar sojojin nan 71 da 'yan bindiga suka kashe.

Image caption Shugaba Muhamadou Issoufou na Nijar da twkwaransa na kasar Faransa Emanuel Macron sun kai ziyara makabartar da aka binne sojojin Nijar da 'yan bindiga suka kashe
Image caption Macron ya kai ziyarar ne a kan hanyarsa ta zuwa kasar Ivory Coast domin yin bikin Kirsimati tare da sojojin kasarsa
Image caption Kasar Faransa ce tsohuwar uwar gijiyar Nijar, wadda ta yi wa mulkin mallaka shekara 61 da suka gabata
Image caption Akwai daruruwan dakarun kasar Faransa a kasar ta Nijar, wadanda suke horarwa tare da taimaka wa wasu rundunonin sojan Nijar din
Image caption Sai dai ziyarar tasa ta gamu da cecekucen daga wasu 'yan Nijar, inda suka ce ba sa maraba da shi sannan suka zargi Faransa da mara wa 'yan bindigar baya
Image caption Wasu 'yan kasar ta Nijar, har wa yau, sun yi kiran da Faransa ta tattara komatsanta ta bar masu kasarasu

Labarai masu alaka