Yadda 'yan bindiga suka kai hari Yobe

Sojin Nigeria
Bayanan hoto,

Har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana duk da ikirarin sojin Najeriya yin galaba kan kungiyar

Rahotanni daga jihar Yobe a Najeriya na cewa wasu da ake tunanin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kusa da garin Damaturu.

Wasu mazauna garin Damaturu da suka tabbatar wa BBC da faruwar lamarin sun ce maharan sun kai harin ne kusan magariba inda suke ta jin karar bama-bamai da musayar wuta, lamarin da ya razana mutanen garin kowa ya boye a gida.

Sun ce an shafe lokaci suna jin karar harbin bindiga kan hanyar Gashuwa, inda suke tunanin 'yan bindigar na kokarin shiga garin ne na Damaturu.

Sun kuma ce suna tunanin 'yan bindigar sun yi musayar wuta ne da jami'an tsaro kafin daga baya komi ya lafa.

Babu dai wani cikakken bayani game da harin, kan ko an samu hasarar rai.

Mataimakin daraktan yada labarai na Rundunar Operation Lafiya Dole, Kaftin Njoka Irabor, ya tabbatar wa da gidan talabijin na Channels faruwar lamarin.

Sannan ya ce jami'an tsaro sun shawo kan lamarin tun a lokacin, har ma hakan ta sa 'yan bindigar suka janye.

An yi ta jin karar harbe-harbe da tashin bama-bamai a sassa daban-daban na birnin, a cewar ganau.

Yadda abin ya faru - Ganau

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa, an fara kai harin ne da misalin karfe biyar na yamma, ba jimawa jami'an tsaro suka halarci wurin kuma suka fara mai da martani ga maharan.

A cewar majiyar maharan ba su shiga cikin gari ba daga wajen gari suke harbe-harbensu, su kuma jami'an tsaron sun girke kayan aikinsu a cikin gari suna harbi zuwa bayan garin.

Suka ce wannan ce hanyar da suke gane harbin ko na wanne bangare ne, yayin da suka daina jin harbi daga bayan gari sai suka tabbatar al'amura sun lafa da misalin karfe takwas din dare kenan.

Hare-haren sun fi karfi ta wajen hanyar Gashuwa inda hedikwatar 'yansanda ta garin, inda kuma nan ne ake gina sabon gidan yarin garin, in ji majiyar.

Wannan dalilin ne ya sa mazauna rukunin gidajen Tijjani Zanna Zakariya da ke kusa da hedikwatar suka fi kowa shiga cikin tashin hankali yayin hare-haren.

Majiyar ta kuma ce mutane da dama da kuma matafiya ne suka kwana a daji sakamakon wannan tashin hankali.

A hannu guda kuma, a ranar Lahadi ne kungiyar IS reshen Afirka ta yamma ta kashe mutum shida tare da sace biyar bayan da suka tare wata babbar hanya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mayakan sun yi ta ware jami'an tsaro ne da kuma ma'iakatan agaji.

Kimanin mayakan ISWAP 30 ne suka tare babbar hanayar da ke kusa da kauyen Gasarwa mai nisan kilomita 100 arewa da Maiduguri babban birnin jihar Barno.

Sun rika tsayar da masu ababan hawa suna tambayarsu katinsu na aiki (ID Card).

Wani direban mota Haruna Ashiru ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "Sun kashe mutum shida sun kuma sace wasu biyar ciki har da mata."