Yadda wutar daji ta tayar da gari a Australia

wutar daji

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban yankin New South Wales Gladys Berejiklian ta ce mummunar wutar daji ta kusan cinye wani gari a Australia

Ta ce babu wani abin da ya rage a garin Balmoral, da ke kudu masu yammacin Sydney, mai yawan al'umma 400.

Jami'an kashe gobara na ci gaba da kokarin yadda za su magance wutar dajin da ke ci gaba da ruruwa a sassan jihohin kasar a yayin da ake cikin yanayi na zafi.

Tun watan Satumba wutar dajin ta kashe mutum akalla tara, tare da cinye daruruwan gidajen mutane da gonaki.

An bukaci mutanen garin Balmoral su kauracewa gidajensu yayin da wutar ke ci gaba da cin gidaje.

Akalla gidaje 86 wutar dajin ta lalata a yankin Adelaide a kudancin Australia, inda kuma aka samu dan shekara 69 ya mutu a gidansa a ranar Asabar.

Yadda wutar dajin ke ci

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images