Turkiyya ta ce ba za ta sake karbar 'yan gudun hijirar Syria ba

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadin cewa kasarsa ba za ta iya hidimar kwararar 'yan gudun hijira daga Syria zuwa kasarsa ba.

Gwamman mutane ne suka tsere zuwa iyakar Turkiyya yayin da ake ci gaba da kai hare-hare kan Lardin Idlib da ke hannun 'yan tawaye a arewa maso yammacin Syria.

A yanzu haka, Turkiyya na bai wa 'yan Syria sama da miliyan uku da ke gudun hijra matsuguni.

Wannan adadi na 'yan gudun hijra shi ne mafi girma a duniya.

Mista Erdogan ya kuma ce kwararar 'yan gudun hijrar zai shafi dukkanin kasashen Tarayyar Turai.

Kusan mutane miliyan uku ne suke zaune a Lardin Idlib, yankin da har yanzu 'yan tawayen da ke adawa da shugaba Bashar al-Assad ke rike da iko da shi.

Abin da Erdogan ya ce

Yayin da yake jawabi a wani bikin bayar da kayututtuka da aka gudanar a birnin Santanbul, Mista Erdogan, ya ce sama da mutane 80,000 daga Idlib ne suka tsere zuwa kan iyakar Turkiyya yayin da sojojin Syria da na Rasha suka tsananta hare-hare a yankin.

"Idan har ba a daina kai hare-hare kan mutanen Idlib ba, wannan adadi zai karu kuma idan hakan ta faru, Turkiyya ba za ta iya rungumar duka 'yan gudun hijrar ba,"a cewar Erdogan.

Ya kara da cewa tasirin da karbar 'yan ci ranin zai haifar, ba wai Turkiyya kadai zai shafa ba, har da kasashen Turai musamman Girka.

Shugaban Turkiyyan ya kuma yi gargadi kan illar rashin kawo karshen rikicin inda ya ba da misali da matsalar 'yan ci ranin da aka fuskanta cikin shekarar 2015 inda sama da mutane miliyan daya suka gudu zuwa Turai.

Ya ce wata tawaga daga Turkiyya ta shirya tsaf domin zuwa Rasha ranar Litinin domin tattauna batun.

Yarjejeniyar tsagaita wuta wadda Rasha da Turkiyya suka jgoranta ta kawo karshen bama-baman da aka kai Idlib cikin watan Agusta sai dai kuma yanzu ana ci gaba da kai hare-haren.

Me Turkiyya take son ya faru?

Turkiyya dai na neman 'yan ci ranin Syria su koma wajen da aka samar wa tsaro a arewa maso gabashin kasar wanda dakarun Kurdawa suka kwace cikin watan Oktoba.

Mista Erdogan ya kuma bukaci goyon baya ga tsarin, yana mai cewa rashin samun goyon bayan zai tilasta masa bude kofa ga 'yan Syrian su shiga Turai.

Kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da Turkiyya take kai wa arewacin Syria sannan kuma kudirin samar da wani waje da aka bai wa tsaro bai samu karbuwa ba a wajen kawayen Turkiyya.

Mista Erdogan ya kuma yi kira ga kasashen Turai da su yi amfani da karfinsu wajen kawo karshen kisan kiyshin da ake yi a Idlib a maimakon kokarin ganin laifin Turkiyya kan matakan da ta dauka a Syria.