Masarautun Kano: Janar Abdussalam zai jagoranci sulhu

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi

Asalin hoton, Tanko Yakasai

Wasu manyan dattawan arewa za su jagoranci sulhu tsakanin masarautar Kano da kuma gwamnatin jihar, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar.

Dattawan sun kafa kwamiti na mutum 10 da ya kunshi Alhaji Adamu Fika, wazirin Fika da Janar Muhammadu Inuwa Wushishi da Farfesa Ibrahim Gambari da Dr Umaru Mutallab da Dakta Dalhatu Sarki Tafida da kuma Sheikh Shariff Ibrahim Saleh

Kwamitin kuma ya kunshi gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi shugaban kungiyar gwamnoni da kuma gwamnan jihar Katsina Aminu Masari.

Sanarwar da kwamitin dattawan ya aikawa BBC ta ce an kafa kwamitin ne domin kawo karshen rikicin tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi wanda suka ce yana barazana ga tsaron jihar da ma wasu jihohin makwabta.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Wazirin Fika ta ce kwamitin zai yi aiki ne tare da cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya domin cimma abin da aka sanya a gaba.

Kuma sanarwar ta ce tuni kwamitin ya fara tuntubar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma mai martaba Sarkin Kano Sanusi na II.

"Sun amince su tsawatar da mabiyansu, don kaucewa fitar da sanarwa ko yi wa wani bangare shagube a shafukan sada zumunta na Internet domin samun damar warware matsalar ba tare da haifar da wani tunzuri ba," in ji sanarwar.

To tun kafin wannan yunkuri na nada kwamitin na Janar Abdussalam, tuni Kungiyar dattawan Arewa ta Northern Elders Forum ta fara wani taron yin sulhu tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi.

Dr. Hakim Baba Ahmed na kungiyar NEF ya shaida wa BBC cewa kasancewarsu dattawa, bai kamata a ce sun yi shiru game da lamarin ba yayin da yake kara kamari.

Ya ce ba su son duk wani abin da zai taba Kano, saboda tsoron kada ya shafi wasu jihohin arewa, yankin da ya ce yana fama da matsaloli na tsaro da talauci.

Rikici tsakanin gwamnatin Kano da masarauta ya sha daukar salo iri-iri tun bayan da gwamna Ganduje ya kirkiro sababbin masarautu hudu - kari a kan ta Kano.

Kuma wannan yunkuri na dattawan yankin arewa na zuwa ne bayan da Sarkin na Kano ya amince da nadin da gwamnan Kano ya yi masa na Shugaban Majalisar Sarakunan jihar.